logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin ya farfado a watanni 6 na farkon shekarar 2021

2021-07-15 20:54:32 cri

Tattalin arzikin Sin ya farfado a watanni 6 na farkon shekarar 2021_fororder_微信图片_20210715204753

Hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluma a yau Alhamis game da yadda tattalin arzikin kasar ke ciki a watanni 6 na farkon bana. Bayan lissafin farko da aka yi, yawan GDPn kasar Sin ya kai RMB yuan triliyan 53.2167, karuwar kashi 12.7% bisa makamancin lokacin bara, ke nan matsakaicin karuwar ya kai 5.3% a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Bisa wannan rahoton tattalin arziki na matsakaicin lokaci, ana iya fahimtar cewa, Sinawa suna sha’awar yin sayayya fiye da lokacin baya, kuma bukatun kasashen ketare kan kayayyakin kasar Sin yana dawowa sannu a hankali zuwa matsayin da suke kafin barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kana masu saka jari na duniya na kara nuna sha’awar zuba jari a kasar ta Sin. Wadannan su ne dalilai uku dake jawo farfadowar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. Kuma wannan yana bai wa kasashen waje damar kara fahimtar karfin kasar Sin na bunkasuwar tattalin arziki da makomar kasar mai kyau a nan gaba.

Kwanan baya, Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya, duk sun kara hasashensu game da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana.

Wannan yanayin shi ne ainihin abin da tattalin arzikin duniya ke bukata, wanda ke neman farfadowa a yanzu haka. Kamar yadda kwararriyar cibiyar bincike kan tattalin arzikin duniya MRB Partners ta nuna a cikin wani rahoto da ta fitar a makon da ya gabata, cewa sakamakon wasu dalilai, ciki har da karfin sayayya, "kasar Sin za ta ba da goyon baya mai karfi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya a nan gaba." (Mai fassara: Bilkisu Xin)