An dade ana muzgunawa musulmai a Amurka
2021-07-15 11:49:21 CRI
Kamar yadda aka sani, kasar Amurka ta kan mayar da kanta a matsayin kasa mafi mai da hankali kan aikin kare hakkin dan adam, haka kuma ta saba da matsa lamba ga sauran kasashe, bisa fakewa da “kare hakkin dan adama”, amma hakika a Amurkan ana muzgunawa musulmai, tare da cin zalin su.
Ana lura cewa, gwamnatin Amurka ta kasa kula da wannan batu, kuma tana tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, bisa fakewa da hakkin dan adam. Kuma matakan da ta dauka sun nuna cewa, ko kadan salon kare hakkin dan adam na Amurka ba shi da nufin kare hakkin al’umma.
Da farko, an lura cewa, gwamnatin kasar Amurka ta dade tana aiwatar da manufar nuna wariyar launin fata, wanda hakan ya zame mata jiki. Duk da cewa, shekaru kusan 20 sun wuce, tun bayan faruwar harin ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, amma har yanzu ana ci gaba da bata sunan musulmai dake rayuwa a Amurka, har ana ci gaba da nuna musu wariya a zaman rayuwar yau da kullum.
Alal misali, suna cikin yanayi na tsoro sakamakon kalubale da sa ido da aka yi musu. A sa’i daya kuma, laifuffukan kin jinin musulmai da ake aikatawa a kasar suna karuwa a kai a kai.
Rahoton da hukumar huldar musulmai ta Amurka ta fitar a shekarar 2018 ya nuna cewa, tun bayan shekarar 2016, adadin kungiyoyin dake adawa da musulmai a Amurka sun karu da ninki biyu. Dan jarida dake aiki a kamfanin dillancin labarai na BBC na Birtaniya Clare Bolderson, shi ma ya lura da yanayin fama da matsin lamba da matasa musulmai na Amurka suke ciki. A don haka ya dauki wani bidiyo mai taken “Musulman Amurka”, inda ya yi bayani kan yanayin rayuwar musulman Amurka, wadanda ake nunawa wariya.
Kana ana nuna wa musulmai wariya kamar yadda ake nuna wariyar launin fata, a cikin fina finai da ake dauka, lamarin da ya kara tsananin raini da kin jini, da fin karfin da ake nunawa musulmai, ko unguwannin da suke rayuwa cikin su. Alal misali, a cikin fina finai mafiya samun karbuwa daga masu kallo, wadanda aka nuna a kasashen Birtaniya, da Amurka, da Australia, tsakanin shekarar 2017 zuwa ta 2019, yawancin wadanda ake sawa su aikata kisan gilla, ko masu kai hare-hare musulmai ne. A don haka, dan wasan fasaha kuma mawakin Birtaniya musulmi Riz Ahmed, ya kafa wani asusu, domin hana bata sunan musulmai a fina finai.
Haka zalika, duk da cewa, Amurka tana kokarin samar da kimar kasa da kasa mai kunshe da samar da zaman jituwa tsakanin kabilu daban daban, a hannu guda kuma an lura cewa, tana aiwatar da manufar mayar da fararen fata kan gaba. Misali a ranar 25 ga watan Satumban shekarar 2017, gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump, ta fitar da umarnin hana shigar musulmai kasar a karo na 3, inda aka hanawa musulmai ‘yan kasashen Iran, da Yemen, da Libya, da Somaliya, da Syria, da Chadi shiga Amurka, saboda gwamnatin kasar tana ganin cewa, wadannan kasashe ba su biyan bukatun kasar Amurka na binciken tsaro, da musanyar bayanai da ake yi wa masu gabatar da rokon neman visa.
Daga baya kuma, wata babbar kotun kasar ta amince da umurnin, bayan jefa kuri’a. Kan wannan batu, kafar watsa labaran kasar Jamus, ta taba wallafa wani rahoto mai taken “Nuna wariya ga musulmai ya riga ya kasance dokar Amurka”, inda aka bayyana cewa, babbar kotun Amurka ta amince da umurnin, lamarin da ya nuna cewa, a karo na farko, an tsara manufar nuna wariya ga musulmai a tarihin kasar.
Haka kuma, an tsara dokar nuna wariya ga musulmai a kasar, duba da cewa, lamarin ya riga ya sabawa ka’idar da aka tsara, a kundin tsarin mulkin Amurka, na samar da daidaito a hakkin ba da kariya, da hakkin yanke hukunci bisa adalci, ga daukacin al’ummun kasar.
Ban da haka, gwamnatin Amurka tana aiwatar da manufar fin karfin domin cin zalin musulmai dake wajen kasar, inda kasar ke yin fuska biyu yayin da take daidaita batutuwan dake shafar musulman ketare. Wato har kullum tana neman samun moriya bisa fakewa da hakkin dan adam.
Tun daga farkon karnin nan da muke ciki, Amurka ta tayar da yake-yake a kasashen Afghanistan, da Syria, da Iraki, bisa fakewa da “yaki da ta’addanci”, a sanadin haka fararen hula musulmai da ba su ci ba ba su sha ba, sama da miliyan goma sun rasa rayukan su, kuma yanzu haka duk da cewa ana fama da cutar COVID-19, amma Amurka ba ta daina kakaba takunkumi ga sauran kasashe ba. Duk wadannan sun sa kasashen sun shiga mawuyancin yanayi mai tsanani.
Ana iya cewa, hakkin dan adama makamin siyasa ne na Amurka, tana yin amfani, da fakewa da shi domin daukar matakan nuna wariyar launin fata, wadanda suke sabawa ka’idojin kasa da kasa. (Jamila)