Shugaban kasar Sin ya aika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Iraki dangane da hadarin gobarar da ta tashi a wani asibiti
2021-07-15 19:38:22 CRI
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Iraki Barham Salih sakon ta’aziyya, dangane da hadarin gobarar da ta tashi a wani asibiti, ta kuma halaka mutane da dama a kasar dake yankin gabas ta tsakiya.
A cikin sakon nasa, Xi, ya ce, a madadin gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa, yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, tare da jajantawa iyalan wadanda suka jikkata.