Kasar Sin ta yi namijin kokari a fannin kare hakkokin kabilun Xinjiang
2021-07-15 16:10:39 CRI
A kwanan nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai kunshe da matakan da mahukuntan Sin ke dauka, don tabbatar da kare daukacin hakkokin kabilun Xinjiang. Taken bayanin shi ne "Martabawa da kare hakkokin daukacin kabilun dake jihar Xinjiang.”
Ga duk wanda ya bibiyi bayanin da kyau, ya kuma ganewa idanun sa irin ci gaban da jihar Xinjiang ta samu, musamman a shekarun baya bayan nan, zai fahimce cewa, akwai daidaito da adalci cikin bayanin da aka gabatar cikin wannan takarda. Ga misali, dukkanin wakilan kasa da kasa, da na sassan al’ummun duniya daban daban da suka ziyarci wannan yanki na Xinjiang, sun sha bayyana irin manufofi na zahiri da suka ga ana aiwatarwa a jihar, da nufin daga darajar rayuwar mazaunanta.
A yanzu haka, jihar Xinjiang na ci gaba da samun bunkasuwa sannu a hankali, cikin shekaru 70 da suka gabata, inda jihar ta samu ingantuwar tsaro, da bunkasar noma, da masana’antu, da ilimi da kiwon lafiya. Jihar ta kuma ci gajiya daga manufofin sauye-sauye da ci gaban rayuwa, bisa hadin gwiwar bangarorin kabilunta, wanda ke rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da lumana.
Shaidun gani da ido sun nuna yadda gwamnatin kasar Sin ke aiwatar da matakai daban daban, na karfafa dokoki, da ingiza ci gaban wannan jiha daga dukkanin fannoni.
Kaza lika, kabilun wannan jiha na ci gaba da hada karfi da karfe, wajen cimma muradun bunkasuwa, da wadata tare. Yayin da kuma fannonin raya siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa, da al’adu ke kara samun tagomashi.
A hannu guda kuma, ana iya ganin yadda hukumomin jihar ke aiwatar da dukkanin matakai, na tabbatar da kare hakkokin dukkanin kabilun wannan jiha bisa doka.
Ko shakka babu, bisa dalilai na zahiri, kamar yadda wannan kundi ya zayyana su a fayyace, kowa na iya gane manufar masu neman bata sunan kasar Sin, ta hanyar fakewa da batun hakkin dan adam Xinjiang. Domin kuwa, babu wani hakki da dan adam zai iya samu, wanda ya wuce kyakkyawar rayuwa, da ci gaban zamantakewarsa. (Saminu Alhassan)