Komai Nisan Jifa Kasa zai fado
2021-07-14 20:32:31 cri
Yanzu dai burin wasu kasashen yamma na neman bata sunan wasu kasashe ta hanyar fakewa da batun kare hakkin bil-Adama ya zo karshe, bayan da zaman hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo na 47, ya amince da kudurin dakile hanyoyin nuna wariyar launin fata, da wasu kasashe ke aikata.
Kafin amincewa da wannan kudiri, mahalarta wannan taro sun nuna damuwa kan yadda har yanzu ’yan Afirka da ’yan asalin Afirka, suke fuskantar kyama da nuna wariyar launin fata a kasashen Amurka da Burtaniya, da Canada, da kasashen dake kungiyar Tarayyar Turai, baya ga mummunan tashin hankali da suke fuskanta a hannun jami’an tsaro da hukumomi na shari’a.
A ’yan shekarun baya-bayan nan ma, an samu karuwar laifukan nuna wariya da tsana, kan ’yan Asiya da ’yan asalin Asiya a kasar Amurka, da Burtaniya da Canada, da Australia, da kasashen dake kungiyar Tarayyar Turai. Abin mamaki shi ne, duk da cewa, bayanai da shaidu na zahiri sun tabbatar da aukuwar irin wadannan danyen aiki a wadannan kasashe, amma abin ka da gwano, wanda ba ya jin warin jikinsa, sai wadannan kasashe suka rika nuna yatsa kan wasu kasashe, wai su ne suke keta hakkin bil-Adama a kasashensu.
Masu fashin baki dai na fatan cewa, amincewa da wannan kudiri mai lakabin "Yayatawa da kare hakkin bil adama, da kare muhimman hakkokin ’yan asalin Afirka daga nuna musu karfin tuwo, da sauran munanan matakan muzguna musu da jami’an tsaro ke yi, ta hanyoyin tabbatar da dokokin da suka shafi hakan." Zai taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.
Ana kuma sa ran kudurin zai kafa wani tsarin aiki, na kwararrun kasa da kasa, mai kunshe da kwararrun jami’an tsaro 3, dake aiki karkashin wasu hukumomin kare doka, da kuma wakilan hukumomin kare hakkin bil adama, wadanda za su rika nazartar irin matakan da gwamnatoci ke dauka kan masu boren kin jinin nuna wariyar launin fata, da yadda ake karya dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil adama. Kaza lika za su ba da gudummawa wajen tabbatar da ganin an gudanar da komai a bayyane, tare da yi wa wadanda aka ci zarafi adalci.
Gabanin wannan, taron ya kuma amince da kudiri kan gudummawar ci gaba, wanda shi ne burin kowace al’umma kana ginshikin warware dukkan matsaloli har a kai ga jin dadin ’yancin dukkan bil-Adama, kudirin da kasar Sin ta gabatar. Wannan shi ne karo na uku da hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta amince da wannan kudiri mai muhimmanci da kasar Sin ta gabatar. A don haka, kasar Sin na fatan kudirin zai taimakawa dukkan sassa wajen cimma matsaya, su kuma hada kai wajen bunkasa ci gaba mai dorewa, ta yadda za a more hakkin bil-Adam na bai daya a duniya, ba wai wata kasa ta rika tsara dokoki ko matakan da za a bi game da batun kare hakkin bil-Adama ba. Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. (Ibrahim Yaya)