logo

HAUSA

A yi kokarin tabbatar da kare hakkokin lafiyar haihuwa na dukkan mutane a kuma ko ina suke

2021-07-14 09:18:03 CRI

Majalisar dinkin duniya ta ayyana ranar 11 ga watan Yulin kowace shekara a matsayin “ranar yawan al’umma ta duniya”. Shekaru 40 bayan da aka samu karin al’umma biliyan uku, yawan al’ummar da ya ninka zuwa biliyan shida. A wannan rana alkaluman kididdiga sun nuna cewa, yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 7.8 a shekarar 2021.

A yi kokarin tabbatar da kare hakkokin lafiyar haihuwa na dukkan mutane a kuma ko ina suke_fororder_210714世界21026-hoto1

A wannan shekara, bikin ya mayar da hankali ne wajen samar da agajin jin kai, don kaiwa ga mata da matasa miliyan 48 dake bukatar jin kai na gaggawa a sassan duniya. Ana bikin wannan rana ce, don kara Ilimintar da jama’a game da batutuwan da suka shafi al’ummar duniya. Kuma hukumar gudanarwar shirin raya kasashe ta MDD ce ta bullo da shirin a shekarar 1989.

A yi kokarin tabbatar da kare hakkokin lafiyar haihuwa na dukkan mutane a kuma ko ina suke_fororder_210714世界21026-hoto2

Bugu da kari, bikin na wannan shekara, yana kokarin mayar da hankali kan muhimmanci batutuwan da suka shafi yawan al’umma, ciki har da dangantakarsu da muhalli da ci gaba.

A sakonsa a bikin wannan shekara, babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bukaci shugabanni da masu tsara manufofi, da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki, da su yi alkawarin tabbatar da kare hakkokin lafiyar haihuwa na dukkan mutane a kuma ko ina suke. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)