Kamata Ya Yi Amurka Ta Kara Mai Da Hankali Kan kubutar Da Jama’arta Da Tinkarar COVID-19
2021-07-14 16:34:44 CRI
Daga Amina Xu
A ‘yan kwanakin baya, kafar yada labarai ta Bloomberg ta Amurka ta fitar da jerin sunayen kasashen da suka yi fice wajen tinkarar cutar COVID-19, inda ta kai Amurka matsaya na daya, yayin da kasar Sin take matsayi na takwas. To, ta yaya Amurka ta iya zama matsayi na farko a wannan fanni? Bloomberg ta gyara mizanan da a kan bi wajen tantance karfin tinkarar cuta ta hanyar cire yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan mamata sakamakon cutar, wadanda yawancin mutane ke ganin cewa, su ne muhimman mizanan tantance karfin tinkarar cuta, amma ta mai da matakan kulle da na killace masu shiga kasa a matsayin matakai maras kyau.
Bisa kididdigar da WHO ta bayar, ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya ya kai fiye da miliyan 180, daga cikinsu miliyan 3.93 sun mutu, kana yawan masu cutar a Amurka kadai ya kai fiye da miliyan 33.71, yayin da yawan mamata ya kai fiye da dubu 600, inda yawan wadanda suka kamu da cutar da yawan mamata ya kai matsayin farko a duniya! Shin hakan ya sa Amurka ta cancanci zama na farko wajen dakile cutar a duniya daga wadannan alkaluma?
A yayin da take yin wannan jeri, Bloomberg ta mai da hankali kan yawan mutanen da aka yi musu rigakafi, don mai da Amurka abin koyi a fannin dakile cutar, wai Amurka ta ingiza yi wa jama’a rigakafi don hana yaduwar cutar, hakan ya sa ta kasance a matsayin farko wajen takile cutar. Idan muka yi la’akari da hakikanin halin da ake ciki, bisa kididdigar da aka bayar kwanakin baya, ya zuwa ranar 12 ga watan Yuli, jama’ar babban yankin kasar Sin fiye da biliyan 1.39 ne aka yi musu rigakafi ba tare da su biya kudi ba, hakan ya sa an farfado da harkokin rayuwar yau da kullum a kasar. Amma, Amurka ta adana allurai har miliyan 30 ba ta baiwa jama’arta kyauta ba, balle ta bayar da taimakonta ga sauran kasashe, musamman ma kasashe maso tasowa. To ga wadannan matakan da Amurka ta dauka, shin ta cancanci zama matsayin farko ta fuskar dakile cutar? Dakta Peter Collignon mai nazarin annoba na kwalejin nazarin aikin likita ta jami’ar ANU ta Austriliya ya ce, lokacin sanyi a arewacin duniya, zai zama wata jarrabawa ga amfanin allurar da aka yi. Haka ne, don yanzu ba wanda zai iya tabbatar da cewa allurar da aka yi a duniya za ta yi amfani mai kyau, don haka tantance karfin tinkarar cutar bisa mizanin yawan wadanda aka yi wa rigakafi, bai dace ba.
Sin tana kan matsayi na takwas a cikin jerin sunayen da Bloomburg ta bayar, inda a ganinta, Sin na daukar matakai masu tsanani na kulle da killace masu shiga kasar, wadanda basu dace ba. Amma, Sin ta dakile yaduwar cutar kan lokaci da ma hana shigar da cutar daga kasashen waje bisa ga daukar wadannan matakai biyu. Abin mamaki shi ne, lokacin da barkewar cutar ta zama gama gari, yawan mamata ya karu sosai, sai Amurka ta fara amfani da matakin kulle da hana shigar baki daga ketare da sauransu, tare da nuna cewa, irin wannan mataki shi ne mataki mafi dacewa da ta bullo da shi wajen hana yaduwar cutar. Amma, yanzu ga shi Amurka ta dauki wadannan matakai a matsayin maras kyau, lalle nuna fuska biyu ne ta yi.
Yanzu duk duniya na matukar bukatar hadin kai wajen tinkarar wannan mumunar annoba, abu mafi muhimmanci shi ne, hadin kan kasa da kasa da rarraba allurar cikin adalci da rage yawan mutanen da ke harbuwa da cutar da yawan mamata sakamakon cutar. Tantance wanda zai zama a matsayin farko wajen dakile wannan cutar ba shi da ma’ana, abin da ya kamata ko wace kasa ta mai da hankali kansa shi ne, tabbatar da tsaron rayuka da zaman rayuwar jama’a. Ba kamar yadda wasu ‘yan siyasa ko kafofi yada labaran Amurka suka yi ba, Gwamnatin kasar Sin ba ta taba shafawa sauran kasashe bakin fenti da hanawa ko yin biris da kokari da ci gaban da sauran kasashe suke samu wajen dakile cutar ba, kuma tana tausayawa jama’ar Amurka wadanda suke shan wahalhalu sanadiyyar cutar. Fatan shi ne wasu ‘yan siyasa da kafofin yada labaran Amurka su daidaita matsayin da suke dauka don sanya muradun jama’a gaba da komai, da tabbatar da rayuka da zaman rayuwarsu bisa iyakacin kokarinsu, a maimakon su yi iyakacin kokarin neman a bayyana su a matsayin kasar da ta yi fice wajen dakile cutar a duniya, sabo da irin wannan suna ba shi da amfani ko kadan wajen tinkarar cutar wadda ke kan ganiyarta a duniya. (Amina Xu)