logo

HAUSA

MDD ta amince da kuduri mai nasaba da shawo kan nuna wariyar launin fata

2021-07-14 09:35:06 CRI

MDD ta amince da kuduri mai nasaba da shawo kan nuna wariyar launin fata_fororder_0714-saminu1-MDD

An amince da kudurin dakile hanyoyin nuna wariyar launin fata, a yayin zaman hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo na 47 a jiya Talata, kudurin da ya tanaji aiwatar da matakan da suka wajaba, don ganin bayan nunawa ’yan asalin Afirka wariyar launin fata.

Kudurin dai na da lakabin "Yayatawa da kare hakkin bil adama, tare da kare muhimman hakkokin ’yan asalin Afirka daga nuna musu karfin tuwo, da sauran munanan matakan muzguna musu da jami’an tsaro ke yi, ta hanyoyin tabbatar da dokokin da suka shafi hakan."

Ana kuma sa ran kudurin zai kafa wani tsarin aiki, na kwararrun kasa da kasa, mai kunshe da kwararrun jami’an tsaro 3, dake aiki karkashin wasu hukumomin kare doka, da kuma wakilan hukumomin kare hakkin bil adama, wadanda za su rika nazartar irin matakan da gwamnatoci ke dauka kan masu boren kin jinin nuna wariyar launin fata, da yadda ake karya dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil adama. Kaza lika za su ba da gudummawa wajen tabbatar da ganin an gudanar da komai a bude, tare da yi wa wadanda aka ci zarafi adalci. (Saminu)