Me ya sa Sin ta samu kyakkyawan sakamakon cinikayyar waje?
2021-07-14 11:28:13 CRI
Jiya Talata, babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ta fidda sabbin alkalumai, wadanda suka nuna cewa, cikin farkon watanni shida na shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da fitar da su ta karu da kashi 27.1 bisa dari idan aka kwatanta da ta makamancin lokacin bara, inda darajarsu ta kai RMB yuan triliyan 18.07, sakamakon da ya kasance matsayin koli a tarihi. Kana adadin ya karu da kashi 22.8 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2019, wato kafin barkewar annobar COVID-19.
Wannan sakamakon cinikayyar waje da kasar Sin ta samu a tsakiyar shekarar 2021, ya nuna yadda kasar ke kokarin karfafa sakamakon da ta samu a baya, a fannonin dakile yaduwar annobar cutar COVID-19, da kuma raya tattalin arziki. Kuma, ya tabbatar da karuwar cinikayyarta da kasashen waje cikin yanayi mai kyau a bana.
Haka kuma, akwai dalilai da dama da suka tabbatar da samun wannan kyakkyawan sakamako a fannin cinikayyar waje. Da farko ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin yanayin zaman karko, ya ba da tabbaci ga karuwar cinikayyar waje. Kamar yadda kafar yada labarai ta Reuters ta kasar Burtaniya ta bayyana, kasar Sin ta fi dukkanin abokan cinikinta sauri, wajen dakile yaduwar annoba, shi ya sa, ta fara samun farfadowar tattalin arziki a farkon shekarar 2020.
Haka yake, a farkon rabin shekarar bana, manyan alkaluman tattalin arzikin kasar Sin dake shafar karuwar masana’antu, da jarin da aka zuba kan kadarori, da kuma saye da sayarwar kayayyakin yau da kullum, sun karu kamar yadda ake fata, kuma bukatun samar da kayayyaki na ci gaba da karuwa cikin kasuwannin kasar, lamarin da ya samar da damammaki ga farfadowa, da karuwar cinikayyarta da kasashen waje.
Ban da haka kuma, karuwar bukatun kasashen waje, sakamakon karuwar mutanen da suka karbi alluran rigakafin cutar COVID-19 a sassan duniya, da farfadowar tattalin arzikin kasa da kasa, ya kara bunkasuwar cinikayyar waje ta kasar Sin.
Kwanan baya, hukumomin kasashen duniya da dama sun daga hasashen karuwar tattalin arzikin duniya, domin farfadowar tattalin arzikin kasa da kasa, ta hanyar inganta karuwar cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa. Cikin farkon rabin shekarar bana, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar da su zuwa kasar Amurka, ya karu da kashi 31.7 bisa dari, kuma adadin hajojin da ta fitar zuwa kasashen mambobin kungiyar EU ya karu da kashi 25.5 bisa dari, sa’an nan, adadin hajojin da ta fitar zuwa kasashen mambobin kungiyar ASEAN ya karu da kashi 27.8 bisa dari.
Bugu da kari, adadin hajojin da ta fitar zuwa Latin Amurka ya karu da kashi 47 bisa dari, yayin da adadin hajojin da ta fitar zuwa kasashen Afirka ya karu da kashi 27.7 bisa dari. Lamarin da ya nuna cewa, muhimmin matsayin kasar Sin a fannin sarrafawa, da samar da kayayyaki cikin kasashen duniya na ci gaba da karuwa.
Haka kuma, raguwar tattalin arziki cikin shekarar 2020, da karuwar farashin hajoji cikin kasuwannin kasa da kasa, sun kasance wasu daga cikin dalilan da suka sa karuwar alkaluman shigo da fitar da kayayyaki tsakanin kasa da kasa.
Bisa kididdigar da aka yi, cikin farkon rabin shekarar bana, karuwar farashin kayayyaki ta ba da gudummawa ta kashi 35.4 bisa dari, kan karuwar adadin kudin shigowar kayayyaki na Sin. Ma’anar hakan ita ce, ya kamata kasar Sin ta dauki matakan dakile hauhawar farashi, domin tabbatar da karuwar cinikayyar waje cikin yanayin zaman karko. Don haka ne ma a kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta riga ta aiwartar da matakan tabbatar da farashin hajoji, domin kare kasuwanni.
Farfadowar cinikayyar waje ta kasar Sin, ba kawai tana tallafa wa kasar Sin ita kanta ba ne kadai, har ma tana tallafa wa kasashen duniya baki daya. Ban da ci gaba da inganta tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa, kamfanonin kasar Sin suna kuma taka muhimmiyar rawa a fannin yaki da annobar COVID-19 a sassan kasa da kasa.
Bisa kididdiyar da aka yi, cikin farkon rabin shekarar bana, kasar Sin ta samar da alluran rigakafi sama da miliyan dari 5 ga kasashe 112, adadin da ya kai kashi 1 bisa 6 na dukkanin alluran rigakafin cutar COVID-19 da aka sarrafa a kasashen duniya. Wanda wannan ya zamo muhimmiyar gudummawar da kasar Sin ta samar wa sassan kasa da kasa, a fannin hadin gwiwar yaki da annoba, da samun farfadowar tattalin arzikin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)