Sanya alluran rigakafin kasar Sin cikin shirin COVAX zai taimaka sosai wajen yakar COVID-19 a duniya
2021-07-14 21:08:41 CRI
Kwanan nan ne kawancen dake samar da alluran riga-kafin cutar COVID-19 a duniya ya sanar da cewa, ya riga ya daddale yarjejeniya tare da wasu kamfanonin kasar Sin biyu, wato Sinopharm da Sinovac, al’amarin da ya nuna cewa, an sanya alluran riga-kafin da kamfanonin biyu suka samar cikin shirin COVAX, kana kuma za su fara samar da alluransu ga shirin COVAX tun daga wannan watan da muke ciki, a wani mataki na taimakawa kasashe masu tasowa yaki da yaduwar cutar.
Wannan wata amincewa ce ta daban da wata hukumar duniya ta yiwa allluran riga-kafin kasar Sin, bayan da hukumar WHO ta sanya wadannan alluran biyu cikin jerin alluran da ake iya amfani da su a matakin gaggawa.
Hakika, an riga an tabbatar da aminci gami da ingancin alluran kamfanonin biyu na dogon lokaci. Yanzu haka, akwai sama da kasashe 100 wadanda suka amince a yi amfani da alluran a kasashensu, yayin da shugabannin kasashe sama da 30 suka riga suka karbi alluran.
Sanya hannu kan yarjejeniyar sayen alluran riga-kafin da kawancen dake samar da alluran riga-kafin cutar COVID-19 na duniya ya yi da kamfanonin biyu na kasar Sin, ya zo a daidai lokacin da kasashe masu tasowa suke matukar bukatar fadada yiwa al’ummominsu alluran, al’amarin da ya sa kasashe dake cikin shirin COVAX za su iya samun alluran ba tare da bata lokaci ba, kuma zuwa watanni shida na farkon shekara mai zuwa, za’a sayi alluran kasar Sin kimanin miliyan 550. Har wa yau, akwai wasu kamfanonin Sin da dama, wadanda suka bayyana niyyarsu ta shiga cikin shirin COVAX, wannan na nuna cewa, za’a kara samun alluran riga-kafin kasar Sin da za su iya bada gudummawa ga ayyukan yaki da yaduwar cutar. (Murtala Zhang)