Sanya Amurka zama kan gaba a duniya a fannin yakar COVID-19 da kamfanin Bloomberg ya yi ya sa mutuncinsa ya zube
2021-07-14 21:37:39 CRI
A bangaren kafafen yada labaran duniya, kamfanin Bloomberg na kasar Amurka ya yi fice a fannin bada rahotanni game da harkokin tattalin arzikin kasa da kasa, wanda ya dade da ikirarin cewa yana bin gaskiya da adalci. Amma kwanan nan ne kamfanin ya fitar da sabuwar takardar jerin kasashen da suka yi fice a fannin yakar cutar COVID-19, inda ya yi wayo har ya sa Amurka ta zama kasa ta farko a duniya a wannan fannin, al’amarin da ya ba wa kowa mamaki a duniya, har ma ya sa mutuncin Bloomberg ya zube kwata-kwata.
Wannan takarda ta baiwa masu amfani da yanar gizo ta Intanet dariya, har sun zargi kamfanin da cewa “ba shi da kunya”. Wasu sun ce, Amurka ta gina dakunan ajiye gawawwaki na wucin gadi sakamakon karuwar yawan mace-mace, amma duk da haka tana kan gaba a duniya. Hakan ya zubar da kimar kamfanin Bloomberg.
Sanin kowa ne cewa, wanda ya kafa kamfanin, Michael Bloomberg, shi ne tsohon magajin garin New York, kana hamshakin mai kudi ne a Amurka. Rahotanni sun ce, tun a shekara ta 2009, wato yayin da Bloomberg ya sanar da shiga takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar democrat, kamfaninsa ya ce ba zai kara bada rahotanni game da binciken Bloomberg shi kansa da sauran ‘yan takara karkashin tutar jam’iyyar democrat ba, amma zai ci gaba da gudanar da bincike kan gwamnatin Trump dake karkashin tutar jam’iyyar Republican. Ke nan za mu iya fahimtar muradun siyasa na kamfanin Bloomberg.
Wannan zamanin da muke ciki, ba zamani ne da kafafen yada labaran kasashen yamma za su iya jirkita gaskiya ba. Gaskiyar magana kuma sanin kowa ne, Amurka ta gaza wajen shawo kan yaduwar cutar, har ma cutar tana kara kamari a kasar. Duk wata kafar yada labarai ta kasashen yammacin duniya da take son jirkita gaskiya, sam ba za ta yi nasara ba kuma ko shakka babu mutuncinta zai zube, kamar kamfanin Bloomberg na Amurka. (Murtala Zhang)