logo

HAUSA

Shigar riga kafin Sinopharm da Sinovac shirin COVAX zai tabbatar da burin da ake da shi na ganin kowa ya samu allurar

2021-07-13 19:02:21 cri

Shigar riga kafin Sinopharm da Sinovac shirin COVAX zai tabbatar da burin da ake da shi na ganin kowa ya samu allurar_fororder_src=http___inews.gtimg.com_newsapp_bt_0_13759798508_1000&refer=http___inews.gtimg

Barkewar sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 na Delta, ya kara jefa tsoro a zukatan al’umma musamman ma kasashe masu tasowa na nahiyar Afrika. Yayin da ake gwagwarmayar samar da riga kafin cutar ga jama’ar kasashe masu karamin karfi, sai kuma ga wata sabuwa, wato bullar sabon nau’in cutar mai saurin yaduwa da ma saurin karya garkuwar jiki.

A jiya ne sakatare janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhnom ya yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su samar da riga kafin ga kasashe masu tasowa. Tun asali dama allurar ba ta game duniya ba saboda yadda masu karfi suka wawushe ta domin yi wa al’ummominsu, har ma suka saye su fiye da yadda suke bukata, ba tare da la’akari da kasashen dake tsananin bukata ba.

A daidai wannan lokaci ne kuma a jiyan, kungiyar kawance domin samar da riga kafi a duniya wato GAVI, ta sanar da cewa, kamfanonin hada magunguna na kasar Sin guda 2, za su samar da alluran riga kafin COVID-19 miliyan 110 ga shirin COVAX. Lallai wannan ya zo a kan gaba, domin dama burin kasar Sin shi ne, ganin allurar ta zama hajjar da dukkan kasashen duniya za su iya sayenta a kan farashi mai rahusa.

Yayin da wasu kasashe suke nuna son kai da ya kai ga samar da wagegen gibi a kan yadda ake rabon allurar, shigar alluran riga kafin kasar Sin na Sinopharm da Sinovac, zai bada kwarin gwiwa ga kasashe masu tasowa na fatan cin galaba kan cutar, ba tare da mayar da hannun agogo baya ba.

Yadda gwamnatin kasar Sin ke karfafa bincike da samar da riga kafin domin amfanin kasashe masu tasowa, abin a yaba ne, domin ta yi abun da wadanda suke ganin manyan kasashe ne, suka gaza aiwatarwa. Har kullum, rashin son kai da kokarin taimakawa kasashe masu tasowa, shi ne ke kai kasar Sin ga kara samun karbuwa. Lallai a yanzu za a ga yiwuwar cimma kyakkyawan fatan ganin kowa, kuma a ko ina ya samu allurar kamar yadda ta dace, domin a gudu tare a tsira tare. (Fa’iza Mustapha)