logo

HAUSA

Sharhi: Nuna Kiyayya Ga Musulmai Al’ada Ce Ta Amurka A Siyasance

2021-07-13 12:55:38 CRI

Jakadan kasar Iran da ke kasar Sin Mohammad Keshavarzzadeh, ya taba bayyanawa, yayin da yake zantawa da dan jaridar Global Times ta kasar Sin, cewa tun bayan shekarar 2001, kasar Amurka ta tada yake-yake a kasashe kimani 80 bisa hujjar wai yaki da ta’addanci, lamarin da ya hallaka mutane fiye da dubu 800, ciki har da fararen hula dubu 330, yayin da aka tilastawa gwamman miliyoyin al’ummun kasashen Afghanistan, da Iraki, da Sham da dai sauransu su barin matsugunansu.

Jakadan ya kara da cewa, idan da gaske Amurka tana lura da hakkin musulmai, to kamata ya yi ta nemi gafara daga wajen wadannan kasashe masu bin addinin musulunci, tare da daina jefa boma-bomai a wadannan kasashe, wanda hakan ya haddasa mutuwar dimbin musulmai.

Furucin jakadan Iran a kasar Sin ya taimaka wajen bayyana ainihin Amurka, a matsayin wadda ta fi azabtar da kasashe masu bin addinin musulunci a zamanin yanzu.

Wasu na da sha’awar sani, tun da Amurka na nuna kin jini ga kasashen musulmai, ko tana kula da hakkokin musulmai ‘yan kasarta? Amma abin takaici shi ne, bayan da aka yi bincike cikin dogon lokaci, an gano cewa, nuna kiyayya ga musulmai wata al’ada ce ta Amurka a siyasance.

Bisa labarin da jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta fitar, an ce a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2019, wani dan Amurka mai suna Patrick Carlineo ya buga waya ga ofishin Ilhan Omar, ’yar majalisar wakilan kasar kuma wata musulma, inda ya yi suka ga ma’aikacin da ya amsa wayar bisa kakkausan harshen cewar, “Shin kana aiki don kungiyar Muslim Brotherhood Emblem? Me ya sa kake taimakawa mata a wajen aiki? Ita ’yar ta’adda ce, zan harbe ta.” Lallai wannan mutumin ya yiwa wata musulma da ke da babban matsayi barazanar kisa ba tare da tsoron komai ba.

To ko me ya sa al’ummar Amurka ke nuna kyamar musulmai kamar hakan? Sakamakon wani binciken da cibiyar nazari ta Pew ta kasar Amurka ta yi a shekarar 2017 ya nuna cewa, yawan musulman da ke zama a Amurka ya zarce miliyan 3 da dubu 450, adadin da ya kai kaso 1.1 bisa na dukkan al’ummar Amurka, kuma kaso 92 daga cikinsu na nuna kyakkyawan fata ga makomarsu.

Ban da wannan kuma, bisa binciken da cibiyar Pew ta yi a shekarar 2019, kaso 82 bisa dari na Amurkawa baligai sun amince da cewa, ana nuna bambanci ga musulman da ke kasar, yayin da kaso 56 bisa dari daga cikinsu na ganin cewa, wannan yanayin da musulmai ke ciki na da matukar tsanani.

Wani abun tambayar shi ne, ko me ya sa musulmai Amurkawa ke cikin yanayi mai tsanani kamar haka? Wannan na da nasaba da yadda Amurkawa ’yan siyasa, da kafofin watsa labaran kasar ke kara gishiri ga dangantakar da ke tsakanin musulmai da ta’addanci, tun bayan harin ta’addanci da ya abku a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001.

Kuma idan ba a manta ba, a farkon shekarar 2017, Donald Trump ya rattaba hannu kan umurnin kayyade shigar baki ’yan kasashen musulmai 7 cikin Amurka, bayan da ya hau karagar mulkin kasar ba da dadewa ba. Ko shakka babu, dalilin da ya sa Trump ya yi hakan shi ne nuna bambancin addini.

Bugu da kari, bayan sa’o’i da dama da kama Patrick Carlineo, wanda ya yi barazanar kashe Ilhan Omar, Trump ya taba ambatar Omar yayin da yake yin jawabi a gaban kawancen Yahudawa ’yan jam’iyyar Republica, inda ya ce, “To, na manta, ba ta son Isra’ila, a yi hakuri, lallai ba ta son Isra’ila, ko ba haka ba?” Kalaman na Trump ya sa Yahudawa ’yan jam’iyyar ta Republica yiwa Omar ba’a. Lamarin da ya shaida sakamakon binciken cibiyar Pew kan yanayin da Amurkawa musulmai ke ciki.

Don haka dai a nan wa yeke nuna bambanci gare su? ’Yan jam’iyyar Republica ne, da Amurkawa fararen fata masu bin darikar Evangelion ta addinin Kirista, da ma sauran jahilai.

Haka zalika ana iya ganin cewa, ba Trump ne kadai ke nuna kiyayya ga Amurkawa musulmai ba, domin kuwa ana iya samun dimbin irinsa a cikin al’umma da ma ’yan siyasa, wadanda ke taimakawa juna wajen shafa wa Amurkawa musulmai kashin kaji.

Ko da yake Amurkawa musulmai na amince da Amurka, amma hakan ba zai hana ’yan siyasa Amurkawa su ci gaba da yada barazanar da musulmai ke yi ga kasar ba. Kamar yadda Hausawa kan ce, ana zaton wuta a makera sai ta bulla a masaka. (Kande Gao)