logo

HAUSA

Babban abun dariya ne a ce Amurka ce take kan gaba a duniya wajen yakar cutar COVID-19

2021-07-13 20:55:33 CRI

Babban abun dariya ne a ce Amurka ce take kan gaba a duniya wajen yakar cutar COVID-19_fororder_A

Zuwa jiya Litinin, mutane kusan miliyan 34 sun kamu da cutar COVID-19, kana sama da dubu 607 sun rasa rayukansu sakamakon cutar a Amurka. Amma duk da haka, sabuwar takardar jerin sunayen kasashen da suka yi fice wajen yakar cutar a duk fadin duniya da kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya fitar, ya nuna cewa, Amurka ce ta farko. Kasar Sin da sauran wasu kasashe da yankuna, wadanda kasa da kasa suka amince cewa sun yi aiki mai kyau a wannan fanni, ba’a yi musu adalci ba.

Tambayar a nan ita ce, me ya sa kasar da a baya bayan nan take yakar cutar, ta zama kan gaba a wannan fannin?

Bloomberg, kamfani ne mafi girma wajen samar da bayanan da suka shafi tattalin arziki da hada-hadar kudi a duniya, wanda tun daga watan Nuwambar bara ya fara fitar da takardar jerin kasashen da suka yi fice wajen yakar cutar COVID-19 a duniya, kuma yawan mutanen da suka kamu da cutar, da yawan mace-mace, gami da hasashen karuwar tattalin arziki na daga cikin muhimman alkaluman da aka yi la’akari da su, wajen jera kasashen. Amma a cikin sabuwar takardar, an canja alkaluman zuwa wasu sabbin fannoni, ciki har da yawan mutanen da suka karbi alluran riga-kafin cutar, da yadda ake daukar matakan kulle masu tsauri, da gudanar da zirga-zirgar jiragen sama da sauransu.

Babban abun dariya ne a ce Amurka ce take kan gaba a duniya wajen yakar cutar COVID-19_fororder_B

Haka kuma, kamfanin Bloomberg ya soke wasu muhimman alkaluma, domin maida kasar Amurka zama a kan gaba a jerin sunayen, har ma ya mayar da wasu matakan dole da aka dauka a matsayin matakai marasa amfani, ciki har da matakan kulle da matakan dakile yaduwar cutar a yayin shige da ficen al’umma.

Mene ne dalilin da ya sa kamfanin Bloomberg ya yi haka? Baya ga matukar yakinin da manyan kafafen yada labaran Amurka suke da shi ga tsare-tsaren kasar, akwai dalilin da ya shafi biyan bukatun siyasa.

Shugaban kamfanin Bloomberg dan jam’iyyar demokuradiyya ne, jam’iyyarsu daya da masu mulki a fadar White House. An kuma ga cewa, an fitar da takardar ce gabannin ranar ‘yanci ta Amurka, al’amarin da ba biyan bukatun ‘yan siyasar kasar kawai ya yi ba, har ma zai taimaka ga maido da mutuncin Amurka wanda ya zube sakamakon gazawar ta wajen yakar cutar COVID-19. (Murtala Zhang)