logo

HAUSA

’Yancin yada labarai na yankin Hong Kong ba zai zama hujjar Amurka wajen tsoma baki cikin harkokin Sin ba

2021-07-12 15:55:42 CRI

’Yancin yada labarai na yankin Hong Kong ba zai zama hujjar Amurka wajen tsoma baki cikin harkokin Sin ba_fororder_210712-sharhi-Maryam-hoto

A ranar 10 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta fidda wata sanarwa mai taken “kawancen ’yancin yada labarai na kafofin watsa labarai”, inda ta zargi gwamnatin yankin Hong Kong na kasar Sin da hannu a hana ’yancin yada labarai.

Amma, gaskiyar batun ita ce, kasar Amurka ta sake neman tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong na kasar Sin bisa hujjar ’yancin yada labarai. Amma, yanzu, kowa ya san burinta, kuma ba za ta cimma burin ba.

Dalilin farko shi ne, matsalar jaridar Apple Daily ta Hong Kong da kasar Amurka ta ambata cikin sanarwar, ba ta da nasaba da ’yancin yada labarai, an tsayar da wannan jarida ne domin ta keta dokar kare tsaron kasa ta yankin Hong Kong. Kuma, kwamitin zartaswa na kamfanin jaridar shi kansa ne ya tsaida kudurin tsayar da fitar da jaridar Apple Daily, ba kamar yadda kasar Amurka ta ce, an tilasta shi ba.

Bugu da kari, ana kiyaye ’yancin yada labarai yadda ya kamata a yankin Hong Kong na kasar Sin, bisa babbar dokar yankin Hong Kong, da dokar kare tsaron kasa ta yankin Hong Kong, da kuma dokar kare hakkin dan Adam na yankin Hong Kong, da ma sauran dokokin da abin ya shafa. Wannan ne kuma ya sa, ’yancin yada labarai na yankin Hong Kong ba zai zama hujjar Amurka, game da tsoma baki cikin harkokin Sin ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)