logo

HAUSA

Masana Da Jami’ai Daga Kasashe Daban Daban Sun Yabawa Tunanin Raya Kasa Na Sin Bisa Tushen Maida Hankali Ga Jama’a

2021-07-12 15:43:22 CRI

A yayin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta Sin, masana da jami’ai daga kasashe daban daban sun yabawa kasar Sin, bisa manyan nasarorin da ta samu a fannoni daban daban, kuma sun yabawa tunanin raya kasa na Sin bisa tushen maida hankali ga jama’a.

Masanin siyasa na kasar Chile Ignacio Araya yana da ra’ayin cewa, dalilin da ya sa Sin ta samu manyan nasarori wajen samun bunkasuwa, shi ne jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS, ta mayar da moriyar jama’a gaban komai. Ya ce, “Jam’iyyar kwaminis ta Sin ta maida moriyar jama’a gaban komai, wanda hakan ya zama ka’ida ta tushe. Idan an lura da hakan, za a iya kara fahimtar kasar Sin, da gano cewa Sin ba kasa ce ta mulkin danniya ba. Domin Sin kasa ce da ta maida hankali sosai ga moriyar jama’a, kana ta yi kokarin cimma burin samun bunkasuwa tare da sauran kasashen duniya.”

A nasa ra’ayin kuwa, daraktan cibiyar nazarin harkokin Sin ta kasar Nijeriya Charles Onunaiju, cewa ya yi JKS, jam’iyya ce da ta zama misali na neman zaman jin dadi ga jama’a. Ya ce, “Halin musamman na jam’iyyar kwaminis ta Sin shi ne, ta yi kokarin tuntubar jama’a da samar da hidima ga jama’a. Idan sauran jam’iyyu suka samar da hidima ga jama’a kamar yadda JKS ke yi, tabbas duniya za ta fi samun kyakkyawar makoma.”

Shi kuwa babban kakakin jam’iyyar PTI ta kasar Pakistan, Saifullah Khan Niazi cewa ya yi, bisa jagorancin JKS, Sin ta warware matsalar talauci, wannan ya shaida cewa, JKS ta yi kokarin kara samarwa jama’ar kasar, har ma dukkanin bil Adama ingantacciyar rayuwa. Don haka Pakistan ke kokarin koyon fasahohin Sin na yaki da talauci. Ya ce, “Babban sakataren JKS Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin, sun yi matukar kokarinsu a fannin cimma burin kawar da talauci. A yanzu muna kokarin koyon fasahohin kasar Sin na yaki da talauci. Muna fatan za mu maida Sin a matsayin misali a fannin aikin kawar da talauci a kasarmu.”

A nasa bangare, mamban jam’iyyar Vatan Partisi na kasar Turkiya Erol Sarigun na ganin cewa, Sin ta zama abun misali a fannin kawar da talauci a duniya. Ya ce, “Sin ta samu manyan nasarori a aikin yaki da talauci, musamman ma a shekaru 5 zuwa 10 da suka gabata, don haka ya kamata kasa da kasa ciki har da Turkiya, su yi koyi da fasahohin Sin a wannan fanni.”

Shi ma shugaban jam’iyyar PF ta kasar Zambia Samuel Mukupa ya ce, bisa jagorancin JKS, babu shakka Sin za ta cimma burinta na zamanintar da kasar karkashin tsarin gurguzu, ta yadda za ta kasance wata kasa mai wadata da demokiradiyya da ma wayewar kai, yayin cika shekaru 100 da kafuwar kasar. Ya ce, “A halin yanzu, Sin ta cimma burin kafa zaman al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni yayin cika shekaru 100 da kafuwar JKS. Yanzu Sin na kokarin neman cimma burin kafa wata kasar zamani mai karfi, yayin cika shekaru 100 da kafuwar kasar. Babu shakka bisa jagorancin JKS, za a cimma wannan sabon buri cikin lokaci.” (Zainab)