logo

HAUSA

Wasu manyan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya sun yaba da muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka

2021-07-13 14:49:34 CRI

Wasu manyan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya sun yaba da muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka_fororder_A

Kwanan nan, wato ranar 1 ga watan Yuli, rana ce ta cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin. Wakiliyarmu Amina Xu ta zanta da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya, ciki har da ministan sufurin jiragen saman kasar, wato Hadi Sirika, da shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan kasar kana mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin cinikayya da kwastam da ‘yancin zirga-zirgar jama’a a majalisar dokokin kungiyar ECOWAS, wato Hon. Aliyu Ibrahim Gebi.

Wasu manyan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya sun yaba da muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka_fororder_微信图片_20210712172958

Minista Hadi Sirika ya yaba da babban ci gaban da kasar Sin ta samu a wadannan shekaru musamman karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis da shugaba Xi Jinping. Shi ma Hon. Aliyu Ibrahimn Gebi ya ce jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da abubuwa nagari da dama da suka cancanci a yi koyi da ita, kuma yana fatan a kara mu’amala tsakanin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Murtala Zhang)