logo

HAUSA

Wane tasiri hadin gwiwar Sin da Masar game da samar da riga-kafin COVID-19 zai yi ga Afirka?

2021-07-12 19:13:27 cri

Wane tasiri hadin gwiwar Sin da Masar game da samar da riga-kafin COVID-19 zai yi ga Afirka?_fororder_微信图片_20210712153905

Tun bayan da aka samu bullar annobar COVID-19 a karshen shekarar 2019, kasar Sin ta sha daukar jerin matakai daban daban da nufin dakile yaduwar annobar a dukkan yankunan kasar, ko da yake, matakan da kasar ke dauka ba su takaita kan bukatu da moriyar kasar kadai ba, har ma ya shafi hadin gwiwar kasar ta Sin da sauran kasashen duniya. Cikin matakai mafiya karbuwa a duniya da kasar ta dauka shi ne batun samar da riga-kafin cutar ta COVID-19 wanda masana suka yi ittifakin shi ne mataki mafi dacewa da zai takawa cutar birki.
Wani batu dake daukar hankalin kasa da kasa musamman kasashe masu tasowa shi ne, batun hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasar Sin da Masar wajen samar da riga-kafin annobar a cikin gidan Masar domin biyan bukatar kasar har ma da kasashen dake shiyyar. Alal misali, a karshen wannan mako hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi maraba da hadin gwiwar tsakanin kasashen Sin da Masar don samar da riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinovac a kasar Masar. A wata sanarwa, wakilin hukumar WHO a kasar Masar, Naeema Al-Gasseer, ya bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Masar wata muhimmiyar nasara ce kuma abin koyi ne ga hadin gwiwar kasa da kasa da musayar fasahohi a duniya, wanda ya bayar da gudunmawa wajen cimma nasarar shirin samar da dauwamammen ci gaba na MDD (SDGs). Kamfanin nazarin kwayoyin halittu da samar da riga kafi na Masar (VACSERA), da kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinovac, sun rattaba hannu a watan Afrilu da nufin yin hadin gwiwa don samar da riga-kafin Sinovac a kamfanin VACSERA na kasar ta arewacin Afrika. A kwanan nan kasar Masar ta shirya bikin murnar samar da alluran riga-kafin kimanin miliyan 1, a kokarin samar da riga-kafin domin biyan bukatun cikin gidan kasar har ma da samarwa ga sauran kasashen dake shiyyar. Al-Gasseer ya ce, hadin gwiwar Sin da Masar a fannin zai taimaka wajen cimma nasarar samar da dauwamammen cigaba na SDGs, wanda ya shafi batun samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma samar da muhimman magunguna da riga-kafi.
A baya bayan nan hukumomin kasar Sin sun bayyana cewa ya zuwa farko farkon wannan wata, kasar ta samar da alluran riga-kafin COVID-19 sama da guda miliyan 480 ga duniya, alkaluma sun nuna cewa ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samar da alluran ga kasashe kimanin 100, ta kuma yi alkawarin samar da kashin farko na allurai miliyan 10 ga shirin COVAX na hukumar WHO. Haka kuma kasar Sin ta yi hadin gwiwa wajen gudanar da bincike da hada riga kafin da samar da shi cikin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa da dama a matsayin wani kudirin kasar na ci gaba da ba da gudummawa wajen ganin kasashe masu tasowa sun samu riga kafin cikin sauki da kuma rahusa domin a gudu tare a tsira tare. (Ahmad Fagam)