logo

HAUSA

Guo Meixin, matashiya ce dake Macau, wadda ke kokarin cimma burinta a yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau

2021-07-12 19:23:34 cri

Shirin raya yankin musamman na Guangdong da Hong Kong da kuma Macau da kasar Sin ta bayar, ya bayyana cewa, za a gina yankin musamman a matsayin wani wuri mai inganci, wanda zai dace da rayuwa, aiki da kuma yawon shakatawa. Yanzu dai, matasa da yawa daga Hong Kong da Macau suna sha'awar yanayin kasuwanci mai kyau da saukin rayuwa da aka samar a wannan yanki na musamman. Kuma sun soma neman ayyukan yi ko raya sana’o’i a babban yankin kasar ta Sin, har sun suke soma sabuwar rayuwar a nan. Guo Meixin, matashiya daga yankin Macau tana daya daga cikinsu.

Kwanan nan, a dakin fasaha da ta kafa, Guo Meixin ta karbi tawagar matasa ta Macau da majalisar cudanya a fannin dokokin shari’a ta Maucau ta shirya. A nan ne, ta bayyana fasahohin da ta koya wajen gudanar da kasuwanci a babban yankin kasar tare da takwarorinta.

“Kudin da ake bukata don fara kasuwanci a Macau suna da yawa, saboda haka ya fi kyau a sami wani wuri mai saukin fara kasuwanci wanda kuma ke iya samar da goyan baya a fannin manufofi.”

An haife Guo Meixin ne, a shekarun 90s, kuma ‘yar asalin yankin Macau ce, ta koma aiki ne a Macau bayan ta kammala karatun ta a Jami’ar Washington a shekarar 2013. Ko da yake tana sha’awar zane-zane tun tana yarinya, amma duk da haka ta zabi aikin kasuwanci sakamakon taimakon iyalinta.

“Ni ma, ina da naci a harkar kasuwanci, baya ga sha’awar fasaha, sannan na yi murabus daga aikina, daga bisani na samu naman damar kafa sana’a da kai na.”

Guo Meixin, matashiya ce dake Macau, wadda ke kokarin cimma burinta a yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau_fororder_gmx

Bayan ta bar aikinta, Guo Meixin ta kaur zuwa birnin Foshan na lardin Guangdong a shekarar 2014. Ba da dadewa ba, ta kaunaci yanayin aiki da rayuwa a nan, kuma ta yi kokarin kafa sana’arta a nan. A yayin bikin baje kolin zane-zane da aka shirya a shekarar 2017, ta hadu da abokin aikinta na yanzu Liang Siting, kuma mutanen biyun da suka dace da juna, nan da nan suka fara kokarin gudanar da sabon shirin kasuwanci tare da wata abokiyar ta.

“A hakika, babu bukatar gabatar da samfuran da yawa yayin fara raya sana’a. Saboda muna gudanar da aikin ba da horo a fannin fasaha, babu misalai da yawa da za mu koya daga wajensu, don haka mu ke ta yin bincike da gwaji a yayin da muke raya sana’armu”

Ba abu ne mai sauki ba, idan ka yi murabus daga wurin aiki, kuma ka je ka fara yin wata sana’a. Tun da ba ka tabbatar da ribar da za ka samu ba kafin kafa sana’ar, nan da nan dakin fasahar da wadannan ‘yan mata ukun suka kafa, ya fada cikin wani yanayi na asara, kuma wata abokiyar kasuwancin, ita ma ta janye daga sana’ar, haka wadanda ke gudanar da kasuwancin tare, suka ragu daga mutane guda uku da farko zuwa mutane biyu a yanzu.

“Gaskiya ne, yawan kudin shiga da muka samu a shekara ta farko da muka soma sana’ar, bai kai abin da muke buri ba, kuma ji dadin wasu lokuta ba, don haka wata abokiyar harkarmu, ta janye daga kasuwanci da muke yi.”

Ita ma Ling Siting, abokiyar kasuwacin namu ta yanzu ta ce,

“Lallai mun fuskanci matsin lamba sosai a lokacin, saboda mu biyu ne muka rage. A wancan lokacin kuma, akwai abubuwa da yawa dake bukatar daidaitawa, ciki har da raba ayyukan da za mu yi, da tabbatar da fannonin da za mu mayar da hankali a kai a nan gaba, da dai sauransu. Ta yaya za mu iya sauya yanayi marasa kyau da muka shiga mu biyu kawai, gaskiya wannan babbar jarrabawa ce a gabanmu.”

A dai dai lokacin da Guo Meixin da Liang Siting suka shiga mawuyacin hali wajen raya sana’arsu, asusun jin dadin jama’a na Shuangchuang na birnin Foshan ya ba su taimakon RMB yuan dubu 500 a matsayin kudin tallafi na matakai biyu, don taimaka musu fita daga mawuyacin halin da suka shiga. Wata jami’a a asusun Tang Xia ta bayyana cewa,

“Galibi harkokin kasuwanci suna fuskantar matsaloli da yawa a farkon kafa su, don haka, akwai bukatar a fara gudanar da ayyuka kamar binciken yanayin kasuwanni da dai sauransu. Sun tsallake kalubaloli daban daban, wannan ya sa muka gano halinsu na musamman a matsayin fitattun masu raya sana’a.”

Guo Meixin, matashiya ce dake Macau, wadda ke kokarin cimma burinta a yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau_fororder_gmx2

A lokaci guda kuma, matasan biyu 'yan kasuwa, suna ci gaba da binciken sabbin hanyoyin gudanar da kasuwanci, don sanya kasuwancinsu kan hanyar da ta dace nan da nan

“Ni da Siting mun canza tsarinmu na kasuwanci da na talla, mun fara kokarin sauya wasu abubuwa da kwasa-kwasan da muka sanya a shagon a zahiri zuwa irin taimakon da muka baiwa wasu kamfanoni wajen tsara ayyukansu, wannan ya sa muka fadada kasuwancinmu a hankali.”

Daga mayar da hankali kan ba da horo a fannin fasaha zuwa yin bincike da hada kai tare da kamfanoni don aiwatar da ayyuka, bayan kusan shekara guda na aiki, a karshe sun samu wasu daidaitattun abokan cinikayya.

A shekarar 2019, domin biyan bukatun abokan cinikayyarsu, sun kaddamar da kwasa-kwasai na kera mafifici mai da’ira irin na gargajiyar kasar Sin, kuma sun cimma babbar nasara.

“A wancan lokacin, ni da Siting mun kai ziyarar aiki birnin Beijing, inda muka ga wani shagon sayar da mafifici mai da’ira, mafifitan dake shagon, suna da salon gargajiya na musamman. Wannan ya sa muka yi tunanin cewa, ko za mu iya hada sana'ar gargajiya da ta zamani domin nuna mafifici mai da’ira, bayan mun dawo daga Beijing, sai muka kaddamar da kwasa-kwasai na saka irin wadannan mafifitai.”

Nasarar da suka cimma na kafa irin wadannan kwasa-kwasai na saka mafifici mai da’ira, ta sanya su kara mayar da hankali kan neman shawarwarin masana al'adun gargajiyar kasar Sin, kuma wasu fasahohin gargajiya na birnin Foshan sun taimaka musu wajen tsarawa.

Yanzu, kasuwancin Guo Meixin da takwararta yana kara samun ci gaba, kuma sun fadada dakin fasahar da suka kafa da farko zuwa dakuna guda hudu a yanzu. Yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau ya sanya Guo Meixin kara jin dadin kasancewarta a yankin, kuma tana daf da cimma burinta a wannan yankin.

“Babban yankin kasarmu babbar kasuwa ce, saboda haka ina ganin cewa, ya kamata matasa daga Hong Kong da Macau su zo babban yankin domin yin bincike da karatu. A ganina, za su iya samun babban ci gaba a nan.”