logo

HAUSA

Me wata rundunar sojojin ruwa mai matukar karfi ta kasar Sin ta kawo wa duniya wasu shekaru fiye da 600 da suka wuce?

2021-07-11 18:13:32 CRI

Me wata rundunar sojojin ruwa mai matukar karfi ta kasar Sin ta kawo wa duniya wasu shekaru fiye da 600 da suka wuce?_fororder_微信图片_20210711181311

Ranar 11 ga watan Yuli ita ce ranar zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin teku ta kasar Sin. Dalilin da ya sa aka kebe wannan rana shi ne, domi tunawa da fitaccen mai aikin ziyara a cikin teku na kasar Sin, mai suna Zheng He, wanda ya fara ziyararsa karon farko a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 1405. Bisa matsayinsa na babban kwamandan rundunar sojojin ruwan kasar Sin a lokacin daular Ming, ya jagoranci wata tawagar da ta kunshi manyan jiragen ruwa fiye da 100, inda suka kai ziyara wuraren dake dab da tekun Indiya har karo 7 cikin wasu shekaru 28, wadanda suka kunshi kasashe da yankuna fiye da 30 na nahiyoyin Asiya da Afirka.

A tsakiyar zamanin daular Ming (1368-1644), kasar Sin wata babbar kasa ce wadda karfin tattalin arzikinta ke kan gaba a duniya. Hakan ya baiwa ziyarar Zheng He tabbaci, a fannonin mutane, da kudi da kayayyakin da ake bukata, gami da fasahohi. Zheng da mutanensa sun yi amfani da manyan jiragen ruwa da aka yi da katako, wadanda tsawonsu daga gaba zuwa baya ya kai kimanin mita 60, kana nauyinsu ya kai kimanin ton 1500. An ce a kowace ziyarar da ya yi, a kan yi amfani da jiragen ruwa fiye da 250, wajen kwashe ma’aikatan jirgin ruwa da yawansu ya kai tsakanin 27000 zuwa 40000. Hakan na nufin, yawan ma’aikata mafi kankanta cikin rundunar Zheng He, ya riga ya kai yawan ma’aikatan da ake samu cikin manyan jiragen ruwa masu dauke da jiragen sama na matsayin Nimitz na kasar Amurka guda 5. Don haka Luis Livases, wani mai nazarin tarihi na kasar Amurka, ya bayyana rundunar Zheng He a matsayin wata fitacciyar rundunar ruwa, wadda ba wanda zai iya karya lagonta, har zuwa lokacin babban yakin duniya na farko.

Sai dai abun da ya fi burgewa shi ne, wannan fitacciyar rundunar sojojin ruwa ta zagaya duniya har sau 7, amma maimakon haddasa tashin hankali da wutar yaki, zaman lafiya, da zumunta, da kuma zama mai wadata ne ta kawo. Cikin shekaru 28 da take ziyara a wurare daban daban, rundunar Zheng He ta tsaya kan manufar kare zaman lafiya don tabbatar da jin dadin jama’ar wurare daban daban, tare da kokarin kulla zumunta da mutanen kasashen da suka ziyarta. Wadannan sojojin kasar Sin sun yi aiki na ‘yan kasuwa, inda suka fitar da kayayyakin kasar Sin irinsu kayayyakin siliki, da na fadi-ka-mutu, da ganyen shayi, da kayayyakin karafa, don musayar kayayyakin sauran kasashe, na turare, da magunguna, da sinadaran da ake bukata wajen hada kayan fadi-ka-mutu, da dai sauransu. Aikin da mutanen Zheng suka yi ya taimakawa karfafa mu’amala a fannin kasuwanci da al’adu tsakanin kasar Sin da sauran kasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka, da yaukaka huldar zumunci tsakanin bangarorin 2. Wasu yake-yake kalilan da rundunar Zheng ta yi, ta yi su ne domin dakile ‘yan fashin teku, da kare zaman lafiya, ko kuma domin mayar da martani kan yadda wasu abokan gaba suka kai hari kan sojojin kasar Sin. Sai dai ko da an kama shugabannin abokan gaba, a kan yafe musu laifuka, da ba su damar komawa gida.

A wani bangare na daban, idan an yi nazari kan tarihin zirga-zirgar jiragen ruwa na kasashen yammacin duniya, za a ga yadda tarihin ke cike da yake-yake da munanan ayyuka na mulkin mallaka, da kwatar albarkatu, gami da kisan kiyashi. Bari mu dauki abun da ya faru a tsibiran Indiya ta yamma a matsayin misali: A shekarar 1496, ‘yan kasar Sifaniya sun kafa wani wurin tsugunar da mutanensu a kasar Haiti. Ya zuwa shekarun 1640, yawan ainihin mazauna wurin ya ragu daga fiye da dubu 60 zuwa 500 kadai. A lokaci guda, mutane ‘yan asalin kasashen Jamaica, da Puerto Rico, da Cuba, wasu fiye da dubu dari daya, an riga an kashe su duka. Ban da wannan kuma, kasashen Turai na Portugal da Sifaniya sun taba rikici da juna kan batun raba duniya, sakamakon yadda suka yi kokarin sanar da mallakar dukkan wuraren da jiragen ruwansu suka isa. Daga baya bisa shiga tsakani da paparoman darikar Katolika ya yi, an shata wani layi daga yankin Norte Pole zuwa yankin Antarctic don raba duniya zuwa yankuna 2, inda yankin gabas ya zama na Portugal, kana yanki na yamma ya zama karkashin mallakar Sifaniya. Ta wadannan batutuwa za a iya ganin rashin imani da kwadayi na masu mulkin mallaka na kasashen yammacin duniya.

Yanzu wasu daruruwan shekaru sun wuce, tsarin duniya ya riga ya sauya sosai, amma halayyar kabilu daban daban kusan ba ta canza sosai ba, ganin yadda wasu kasashen yammacin duniya ke ci gaba da kokarin cin zarafin sauran kasashe, ta hanyar nuna fin karfi da karfin tuwo. Yanzu sun fara yin amfani da matakan kasuwanci wajen kwatan albarkatu, da yin amfani da dabarun siyasa da al’adu wajen shawo kan sauran al’ummu, har ma suna amfani da karfin soja wajen hambarar da gwamnatocin sauran kasashe don ta da rikice-rikice a can. Yayin da a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan manufofinta na kare zaman lafiya, da neman ci gaban tattalin arziki, da hadin gwiwa, gami da tabbatar da moriyar juna. Inda ta nuna kin amincewa ga ra’ayin nuna kasaita da fin karfi, kana tana kokarin tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga ‘yan Adam baki daya a duniya. Har kullum kasar Sin tana kokarin samar da gudunmowa ga yunkurin kare zaman lafiya, da neman ci gaba, da tabbatar da tsari da oda a duniyarmu.

Abubuwan da suka faru a tarihin dan Adam sun nuna mana cewa, ko da yake mulkin danniya da karfin tuwo sun iya haifar da riba ga wasu kasahse cikin wani guntun lokaci, ba za su iya hana yunkurin mutane na kokarin bijerewa mutanen da suka ci zarafinsu ba. Saboda haka, tsarin mulkin mallaka na Turawa ya rushe bayan babban yakin duniya na biyu, inda kasashe da yawa na nahiyoyin Asiya da Afirka da Latin Amurka suka kwatar wa kansu ‘yanci. Bisa wannan lamari ne za mu iya hasashen makomar kasashe masu aikata mulkin danniya da fin karfi a duniya. (Bello Wang)