logo

HAUSA

Kara Sanya Takunkumi Da Kasar Amurka Ke Yi Ba Zai Tsoratar Da Kowa Ba

2021-07-09 13:07:21 cri

Fadar White House ta kasar Amurka ta sanar a ranar 7 ga wata cewa, wai za ta tsawaita "dokar ta bacin da aka ayyana dangane da halin da Hong Kong ke ciki", da ci gaba da sanya takunkumin da ke da alaka da Hong Kong. Wannan ya nuna cewa, gwamnatin Amurka mai ci, tana ci gaba da bin mummunar manufar siyasa ta tsohuwar gwamnatin kasar, da nufin ci gaba da tsoma baki a cikin harkokin Hong Kong, da ma harkokin cikin gidan kasar Sin.

Kasar Amurka ta yi ikirarin cewa, babban dalilin da ya sa ta yanke wannan shawara shi ne, wai matakan da ke da nasaba da Hong Kong da kasar Sin ta dauka, na ci gaba da "yin barazana" ga tsaron kasa da manufar diplomasiyya da kuma moriyar tattalin arzikinta. Kalaman na Amurka, tamkar mayar da fari baki ne. Hong Kong wani yanki ne na musamman dake karkashin mulkin kasar Sin, gudanar da harkokin Hong Kong da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ke yi, harkar cikin gida ne na kasar, ina ruwan Amurka? Kuma wace barazana hakan ke da shi ga tsaron Amurka? Kwanan baya, "Takardar Bayani Game Da Kamfanonin Amurka a Sin", wadda Kungiyar 'Yan Kasuwan Amurka da ke kasar ta Sin ta fitar ta nuna cewa, kashi biyu bisa uku na kamfanonin Amurka sun nuna shirinsu na kara saka jari a kasar Sin. Shin kamfanonin Amurka za su saka hannun jari a wata kasar da ke "barazana" ga kasarsu?

A hakika dai, idan ana maganar "barazana", abin da ake gani shi ne, Yadda Amurka ta dade tana goyon bayan masu adawa da gwamnatin kasar Sin da masu tayar da rikice-rikicen a yankin Hong Kong, da kuma kokarin bata sunan kasar Sin. Wannan shi ne ainihin babbar "barazana" ga ikon mallakar kasar Sin, da tsaro da kuma ci gaban kasar! Abin da ke nuna cewa, wai ci gaba da saka takunkumin da ya shafi Hong Kong ya kara fallasa yunkurin wasu ‘yan Amurka na tayar da rikici a Hong Kong da matsawa kasar Sin lamba.

Kara Sanya Takunkumi Da Kasar Amurka Ke Yi Ba Zai Tsoratar Da Kowa Ba_fororder_锐评1

Amma, ko ma mene ne, matakan da suka dauka ba za su yi nasara ba. Yau a cikin Hong Kong, ba su da wani sarari na ci gaba da aikata duk wani danyen aiki.

A cikin shekarar da ta gabata, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta aiwatar da Dokar Tsaron Kasa ta Hong Kong da kyautata tsarin zaben na Hong Kong, matakan da suka taimaka wajen kiyaye tsaron kasa yadda ya kamata, da maido da zaman karko a yankin, kana da kiyaye hakkokin mazauna Hong Kong a fannoni daban daban. Yanzu an shiga sabon yanayi mai kyau a yankin na Hong Kong.

A 'yan kwanakin da suka gabata, a zama na 47 na majalisar Kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, matashiya daga yankin Hong Kong mai suna Chen Yingxin ta gabatar da jawabi a matsayin wakiliyar kungiyoyi masu zaman kansu, inda ta ce, al’ummar Hong Kong na maraba da aiwatar da Dokar Tsaro ta yankin, saboda dokar ta ba da tabbaci ga ’yancinsu na rayuwa ta yau da kullum. Tana kuma fatan kasashen yamma za su fahimci cewa, matasa a Hong Kong suna kaunar kasarsu da yankin Hong Kong, kuma suna adawa da tsoma bakin da kasashen waje suka yi a yankin.

Kara Sanya Takunkumi Da Kasar Amurka Ke Yi Ba Zai Tsoratar Da Kowa Ba_fororder_锐评2

Lokacin da Amurka ta sanya takunkumi a kan Hong Kong shekara guda da ta gabata, ta taba bayyana cewa, wai masu jari da dama za su janye daga Hong Kong. Amma sakamakon shi ne, a cikin shekarar da ta gabata, yankin Hong Kong na kara karfinsa na jawo jarin waje saboda aiwatar da Dokar Tsaro ta Hong Kong. Kididdiga ta nuna cewa, yawan kudaden da suka kwarara zuwa Hong Kong a bara, ya kai dala biliyan 50. A watanni uku na farkon shekarar bana, GDP na Hong Kong ya karu da kashi 7.9% idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Asusun ba da Lamuni na Duniya ya bayar da rahoto a 'yan kwanakin da suka gabata, inda ya sake tabbatar da matsayin Hong Kong a matsayin cibiyar hada-hadar kudi ta duniya.

Ci gaban yankin Hong Kong ya dogara ne da gwagwarmayar mazauna wurin, da kuma goyon baya mai karfi daga babban yankin kasar Sin, kuma ba ta taba dogaro da kyauta ko sadaka daga kasashen waje ba.

Kasar Amurka na neman tsoratar da Hong Kong ta hanyar saka takunkumi, ba ta cimma burinta ba a baya, haka kuma ba za ta cimma wannan buri a yanzu da ma nan gaba ba. (Mai fassara: Bilkisu)