An gano wata halittar dan Adam na zamanin da a Isra'ila
2021-07-09 09:23:24 CRI
Bincike na nuna cewa, duwatsun kasusuwan dan Adam da aka gano a kasar Isra’ila, na wata halittar dan Adam ne na zamanin da, wadanda suka rayu a duniyarmu shekaru dubu 120 zuwa dubu 140 da suka gabata. Masu ilmin kimiyya suna kiran wannan halitta da suna Nesher-Ramla.