logo

HAUSA

Wasu kasashe ba su cancanci koyarwa wasu yadda ake kare hakkin bil adama ba

2021-07-09 21:17:20 CRI

Wasu kasashe ba su cancanci koyarwa wasu yadda ake kare hakkin bil adama ba_fororder_aus

Jiya Alhamis, an duba rahoton yanayin kare hakkin bil adama da kasar Australia ke ciki, a karo na uku a yayin taron majalisar kiyaye hakkin bil adama ta MDD karo na 47, inda kasashen Sin, da Rasha, da Syria, da wakilan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD suka nuna damuwa matuka, kan laifin keta hakkin bil adama da aka aikata a kasar ta Australia, lamarin da ya nuna cewa, kasar Australia wadda ke mayar da kanta a matsayin malamar koyarwa saura yadda ake kare hakkin bil dama, ta sha aikata laifuffukan dake shafar keta hakkin bil adama.

A cikin shekaru daruruwa da suka gabata, gwamnatin Autralia tana ci gaba da cin zarafin al’ummun kasar, wadanda suka rayu a kasar tun tuni. Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a shekarar 1788, bayan da Turawan Birtaniya suka sauka a Autralia a karo na farko, gaba daya mutanen dake rayuwa a kasar sun kai wajen miliyan 1, amma ya zuwa farkon karni na 20, adadin bai kai dubu 20 ba, kuma a yanzu haka adadin bai wuce kaso 3.3 bisa dari cikin daukacin al’ummun kasar ta Autralia ba, yayin da adadinsu wadanda ke fursuna a cikin kasar ya kai kaso 28 bisa dari.

A watan Nuwamban bara, an gabatar da labarin cewa, sojojin kasar Autralia dake aiki a kasar Afganistan, sun kashe fararen hulan kasar, wadanda yawan su ya kai 39, laifin da ya gamu da kakkausan suka daga sassan kasa da kasa.

Hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wadda ke koyarwa saura yadda ake kare hakkin bil adama, ita kanta tana keta hakkin bil adama. (Jamila)