Ya Zama Wajibi Kasashen Afirka Su Kara Kaimin Rigakafi A Gabar Da Ake Samun Bazuwar COVID-19 Nau’In Delta A Sassan Nahiyar
2021-07-08 16:52:14 CRI
Daga Saminu Alhassan
Rahotannin baya bayan nan na tabbatar da karuwar adadin mutane dake harbuwa da cutar COVID-19 nau’in Delta, a wasu kasashen Afirka da dama, lamarin da ya sanya kwararru ke nuna fargabar cewa, hakan na iya haifar da mummunar barna ga nahiyar.
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ya zuwa makon karshe na watan Yuni da ya shude, wannan nau’in cuta ya shiga kasashe 3 cikin 5 dake sahun gaba, a yawan masu harbuwa da annobar COVID-19. Kaza lika WHO ta ce cikin mutane da aka yiwa gwajin cutar a Uganda, kaso 97 bida dari na dauke da nau’in na Delta, yayin da wannan adadi ya kai kaso 79 bisa dari a janhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Har ila yau, wasu masana kimiyya sun bayyana sakamakon binciken da suka yi a kasar Kenya, wanda ya nuna cewa nau’in Delta na COVID-19 na maye gurbin nau’oin Alpha da Beta da aka sha fama da su a baya. Kuma nau’in na Delta yana da hadarin gaske, ta fuskar saurin yaduwa da kuma jikkata wadanda suka harbu da shi.
Ko shakka ba bu, dukkanin wadannan alkaluma na sakamakon binciken kwararru, na nuni ga tsananin bukatar da ake da ita, ta maida hankali ga gaggauta aikin rigakafi a sassan nahiyar Afirka, domin kaucewa asarar rayuka, da jikkatar mutane masu yawa a nahiyar.
Yanzu haka dai gwamnatocin kasashen Afirka da dama sun himmatu, wajen aikin samar da rigakafi, da kuma yiwa al’ummun su alluran, ko da yake aikin na fuskantar kalubale na rashin isassun alluran daga sassan dake samar da su, da kuma yadda a wasu yankunan nahiyar, mutane ke kauracewa karbar rigakafin, duk kuwa da wayar da kai da ake ta faman yi kan sahihancin alluran.
Da yake dukkanin kwararru sun amince cewa, dole ne a samar da rigakafin COVID-19 ga daukacin sassan duniya, idan har ana fatan ganin bayan cutar gaba daya, ke nan akwai bukatar kara azama wajen samar da isassun rigakafin ga kasashe masu tasowa, musamman karkashin shirin nan na COVAX, da kuma irin gudummawar da Sin ke samarwa kasashe masu tasowa, ta tallafin rigakafin.
A daya hannun kuma, wajibi ne mahukuntan kasashen Afirka, su zage damtse wajen wayar da kan jama’a, game da muhimmancin karbar rigakafin wannan cuta, ta yadda za a kai ga dakile daduwar wannan nau’i na Delta, da ma sauran nau’oin COVID-19 a kan lokaci.(Saminu Alhassan)