Kungiyar ba da taimakon jinya ta Sin dake Equatorial Guinea na tsayawa kan sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka
2021-07-08 14:55:12 cri
Bana shekaru 50 ke nan da kasar Sin ta aika kungiyar ba da jinya zuwa kasar Equatorial Guinea. A cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, kungiyar ba da jinya ta kasar Sin dake Equatorial Guinea, ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ba da gudummawa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma a fannin kiwon lafiya ta Sin da Afirka.
Tun daga shekarar 1971, lardin Guangdong na kasar Sin ta soma daukar nauyin tura kungiyoyin ba da taimakon jinya zuwa kasar Equatorial Guinea, ya zuwa yanzu, ta riga ta tura rukunoni 31 da suka kunshi mambobi 586 na kungiyar. A ranar 13 ga watan Janairun wannan shekara, kungiyar ba da taimakon jinya ta 31 ta isa Malabo, babban birnin Equatorial Guinea. Sakamakon hali mai tsanani da wurin ke ciki na tinkarar annobar numfashi ta COVID-19, ‘yan kungiyar suna bukatar daukar matakan kariya a yayin da suke gudanar da ayyukansu na ba da jinya na yau da kullum.
Likitan da ba ya aikin tiyata Lin Xianjie ya bayyana cewa,
“Yanayin dakunan kwanciya na wurin ba su da kyau, wasu dakunan kananan ne kuma babu iska. Ma’aunin yanayi zafi a dakunan yana haura sama da digiri 30 a ko wace rana, kuma babu na’urar sanyaya daki kuma fankokin kadan ne. Bayan aiki na tsawon yini, muna shiga hali kamar mun fito a cikin ruwa, tufafinmu duk sun jike, safan hannumu kuma sun cika da ruwa.”
A shekaru 20 da suka gabata, Shi Yuqi, likitar kula da yara kanana daga asibitin Bo'ai na birnin Zhongshan na lardin Guangdong, wadda ta kasance mambar kungiyar ba da jinya ta kasar Sin dake Equatorial Guinea, ta taba aiki a asibitin Bata na kasar ta Equatorial Guinea. Bayan shekaru 20, abokin aikinta Liang Senquan, ya sake zuwa nan bayan ita, ya gano cewa, tsohuwar abokiyar likita Shi Yuqi ita ma an yi mata maraba da zuwa wurin.
“Har yanzu ina tuna lokacin da na isa asibitin Bata, don karbar aikin a ranar farko, akwai wata likita a cikin sashenmu, wadda ke sanye da tsohuwar riga ta kungiyar ba da jinyarmu. Bayan da muka tattauna mun fahimci cewa, ita ce likita Nina da darakta Shi Yuqi ta ambata a baya. Da gangan ta sa tsohuwar farar rigar kungiyarmu don ta yi mana maraba da zuwa, sai na ji kamar ta marabci tsoffin abokanta.”
Abotar da ke tsakanin Sin da Equatorial Guinea tana iya ratsa duwatsu da tekuna kuma tana iya jure jarrabawa. A yayin bikin sharar kaburbura na Qingming, wato bikin gargajiyar kasar Sin na bana, mambobin kungiyar ba da jinya ta kasar Sin dake Equatorial Guinea, sun ara tutocin kasar Sin da furanni a kabarin likita He Xianjie da ke karkarar birnin Bata, don gudanar da wani biki mai sauki, domin tunawa da shi. Likita Liang Senquan ya bayyana cewa,
“Marigayi He Xianjie, shi ne likitan kula da ido a kungiyar ba da jinya ta kasar Sin karo na 6 dake kasar Equatorial Guinea, kuma dan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya mutu ne bayan ya yi fama da zubar jini na kwakwalwa a ranar 30 ga Maris a shekarar 1978, sakamakon aiki fiye da kima. A lokacin, shi saurayi ne, da shekarunsa ba su wuce 42 ba.”
A wancan lokacin, labarin mutuwar wannan likitan kasar Sin, ya firgita dukkan kasar Equatorial Guinea, dubun-dubatar mutanen yankin ne suka kai shi makwanci, shugaban kasar da uwargidansa ma sun halarci jana'izar tare da tuna kabarin da za a binne shi. Daga baya, kowane rukuni na kungiyoyin likitocin kasar Sin da suka zo Equatorial Guinea za su ziyarci kabarin likita He Xianjie yayin bikin Qingming.
Tun bayan barkewar annobar COVID-19 a bara, kasashen Sin da Equatoria Guinea, suke yin hadin kai don tinkarar annobar. A watan Faburairun bara, wato lokacin da birnin Wuhan na kasar Sin ya yi fama da annobar, gwamnatin kasar Equatoria Guinea, ta ba da tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 2 ga kasar Sin. A watan Mayun shekarar kuma, gwamnatin kasar Sin ta aika da tawagar kwararru likitanci zuwa kasar don ba da taimako, a bana kuma ta samar da tallafin alluran riga kafi har sau biyu ga kasar daya bayan daya. (Bilkisu)