logo

HAUSA

Dokar tsaron HK tana tabbatar da moriyar mazauna yankin

2021-07-08 21:07:13 CRI

Dokar tsaron HK tana tabbatar da moriyar mazauna yankin_fororder_hk

Duk da cewa, wasu rukunonin ‘yan adawa da kasar Sin na kasashen yamma, suna sukar dokar tsaron yankin Hong Kong, amma sakamakon da aka samu bayan da aka fara aiwatar da dokar kafin shekara daya da fara aiki da ita, ya shaida cewa dokar tana taka babbar rawa wajen tabbatar da moriyar yankin, da kuma moriyar mazauna yankin.

Da farko, dokar tana hukunta mutanen kalilan, wadanda suke tayar da hankali a yankin kadai, haka kuma tana ba da kariya ga yawancin mazauna yankin a cikin shekarar da ta gabata, wato tun bayan da aka fara aiwatar da ita, inda aka maido da doka da oda a yankin Hong Kong yadda ya kamata.

Kana, matsayin Hong Kong na cibiyar hada-hadar kudi da zirga-zirgar jiragen sama, da cinikayya ta kasa da kasa yana kara karfafuwa a karkashin kariyar dokar tsaro ta Hong Kong, a don haka muhallin kasuwancin yankin ya kyautata, har ma jarin da aka zuba a yankin ya karu.

Haka zalika, shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14 da aka kaddamar a kasar Sin a farkon bana, ya samar da sabon izini ga ci gaban Hong Kong, ko shakka babu muhalli mai tsaro sakamakon aiwatar da dokar tsaron yankin, ya samar da sharadi mai inganci ga yankin, yayin da yake kokarin shiga babban shirin ci gaban kasar ta Sin.  (Jamila)