Yabon Gwani Ya Zama Dole
2021-07-07 16:55:42 CRI
Daga Ibrahim Yaya
A ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara ce, JKS ta yi bikin cika shekaru 100 cif da kafuwa, Kuma tun wannan lokaci har zuwa yanzu, shugabannin jam’iyyun siyasa da gwamnatocin kasashen waje, ke ci gaba da aiko sakonnin taya murnar cikar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin shekaru 100 da kafuwa.
A cikin sakonnin da suka aiko, kodai ga babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ko kwamitin tsakiya na JKS, jagororin sun tabo irin manyan nasarori da babbar gudummawar da JKS ta baiwa duniya a cikin shekaru 100 da suka gabata, musamman tun lokacin babban taron jam’iyyar karo 18, inda suka bayyana tabbacin cewa, JKS za ta kara cimma nasarori a nan gaba.
JKS na fara ne da mambobi kalilan, inda yanzu ta zama babbar jam’iyya mai karfi da ma yawan mambobi a duniya, jam’iyyar da ta yi nasarar tsame al’ummar Sinawa baki daya daga kangin talauci, tare da gina al’ummar mai matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni.
A sakonsa, shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani cewa ya yi, bayan shekaru 100 na gwagwarmaya da sadaukar da kai, JKS ta yi nasarar magance galibin manyan kalubaloli tare da jagorantar kasar Sin, zuwa kasa mai karfi a duniya.
Shi kuwa shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera cewa ya yi, al’ummar kasarsa da ta Sin, kansu a hade yake kuma ‘yan uwan juna ne, sun kuma himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, da bunkasuwa da samar da farin ciki ga al’ummominsu. Sun kuma kafa al’umma mai kyakkyawar makoma. Shugaba Touadera ya ce, yana fatan yin amfani da bikin cikar JKS shekaru 100 da kafuwa, a matsayin wata dama, ta kara inganta da zurfafa hadin gwiwar abokantaka tsakanin kasashen biyu.
Shi ma shugaban Benin Patrice Talon, a nasa sakon ya bayyana cewa, cikar JKS shekaru 100 da kafuwa, zai bude wani sabon babi na farin ciki da haske ga al’ummar Sinawa da ma bil-Adama baki daya,yana mai cewa, a shirye Benin ta ke ta zurfafa alaka da musaya a fannoni daban-daban, da kara kawo alheri ga jama’ar kasashen biyu da ma duniya baki daya. Wadannan kadan ne daga cikin irin sakonnin da kasar ke samu, biyo bayan tarin nasarorin da ta samu karkashin jagorancin JKS, nasarorin da suka amfani duniya baki daya.
Tun farkon kafuwarta, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi alkawarin cewa, ya zama wajibi a mayar da moriyar al’ummun kasar a gaban komai, kuma a cikin shekaru 100 da suka gabata, al’ummun Sinawa suna yi kokarin gina sabuwar kasar Sin karkashin jagorancin JKS, haka kuma sun yi nasarar gina kasa mai tsarin gurguzu, ta hanyar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare, babban burin JKS na gaba, shi ne samar da wadata ga al’ummun kasar.
JKS tana son ci gaba da hada kai da jam’iyyu da kungiyoyin siyasu na duniya, wajen kara inganta ci gaban dan Adam, a kokarin kara ba da sabuwar gudummowa ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam da samun duniya mai kyau da kowa zai ji dadin zama a cikinta
Don haka, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Xi Jinping ya jaddada cewa, duk mai yunkurin gurgunta huldar dake tsakanin JKS da al’ummun kasar Sin, ya kwana da sanin cewa, ba zai yi nasara ba.(Ibrahim Yaya)