Ya dace jam’iyya ta yi kokarin samar da wadata ga al’ummun kasa
2021-07-07 19:30:06 CRI
Jiya Talata babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, yayin taron shugabannin JKS da jam’iyyun kasa da kasa, inda ya bayyana cewa, “Bisa matsayinta na muhimmin karfin ingiza ci gaban bil Adama, ya dace ko wacce jam’iyya ta sauke nauyi bisa wuyanta, domin samar da wadata ga jama’a, da kuma ciyar da bil Adama gaba yadda ya kamata.”
A halin da ake ciki yanzu, bil Adama na fuskantar hadurra da kalubaloli da dama, a don haka ya dace jam’iyyun kasashe daban daban, su yi namijin kokari domin daidaita kalubalolin, tare kuma da biyan bukatun al’ummun kasa da kasa. Ana kuma sa ran taron kolin jam’iyyun da JKS ta kira jiya, wanda ya kasance irin sa mafi girma zai taka rawarsa a bangaren.
Yayin taron, babban sakatare Xi Jinping ya yi tattaunawa da shugabannin jam’iyyu da kungiyoyin siyasa sama da 500, da wakilan jam’iyyu da bangarori daban daban sama da dubu 10, da suka zo daga kasashe fiye da 160, kan batu game da samar da wadata ga jama’a da nauyin dake bisa wuyan jam’iyya, kuma ya gabatar da dabarun JKS a fannoni biyar, wadanda ke kunshe da ba da jagoranci, da cimma matsaya guda, da ingiza ci gaba, da karfafa hadin gwiwa, da kuma kyautata aikin gudanar da harkokin kasa.(Jamila)