logo

HAUSA

Kawowa Jama’A Alheri Nauyi Ne Dake Wuyan Jam’Iyyu

2021-07-07 21:33:45 CRI

Kawowa Jama’A Alheri Nauyi Ne Dake Wuyan Jam’Iyyu_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_news_crawl_7_w550h257_20210707_d3f5-ksmehzs8345790&refer=http___n.sinaimg

Daga Amina Xu

Jiya Talata 6 ga wata, an kira taron koli tsakanin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) da jam’iyyun kasa da kasa ta kafar bidiyo, inda shugabannin jam’iyyu da kungiyoyin siyasa fiye da 500, da kuma wakilan jam’iyyu daban-daban fiye da dubu 10 daga kasashe fiye da 160, suka halarci taron, wanda aka yiwa lakabi da “Kawowa jama’a alheri: Nauyi ne dake wuyan duk wata jam’iyya”.

Wailan kasashe masu tarin yawa sun halarci taron bisa gayyatar kasar Sin, kuma galibinsu manyan shugabannin jam’iyyun kasa da kasa ne, abun da ya bayyana babban muhimmanci da suke dorawa game da JKS.

Sin ta samu ci gaba mai armashi karkashin jagorancin JKS. A gani na wannan shi ne dalilin da ya sa wadannan shugabanni suka maida wannan taro matsayin wani babban dandali, na leka manufofin da Sin take aiwatarwa, da suka kai ta ga samun irin wadannan nasarori.

A yanzu cutar COVID-19 na kan ganiyarta a duniya, kuma duniya ta gaza samun karfin farfado da tattalin arzikinta, kuma ra’ayin rufe kofa da na kyamar kwararru, da fitattun mutane na wata al'umma na kunno kai a wasu kasashe. Kasashe daban-daban da jam’iyyunsu na yin kokari amsa wannan tambaya: cewa Me ya faru a duniya, yaya za a yi nan gaba, ina makomar duniya?

JKS ta kara yin hadin kai da mu’ammala da jam’iyyun kasa da kasa, a daidai wannan lokaci da ake fuskantar mawuyancin hali, ba shakka hakan zai samar da basirarta da hadin kai da sauran kasashe, wajen warware wadannan matsaloli da ake fuskanta.

Wannan shekara ita ce ta cika shekaru 100 da kafuwar JKS. Na kuma zanta da mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin cinikayya da kwastan da ‘yancin zirga-zirgar jama’a a majalisar dokokin ECOWAS, kana shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan kasar Najeriya Aliyu Ibrahim Gebi, a matsayin wani shugaba na kungiyar kasa da kasa, ya kan nazarci manufofin jam’iyyu, da ci gaban tattalin arziki da al’umma da ake samu. Ya kuma nuna sha’awar manufofin JKS kwarai da gaske. Ya bayyana min cewa, tun kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin har zuwa yanzu, Sin ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a matsayi na biyu a duniya, daga kasa dake fama da talauci da koma baya, wanda ya kasance wata babbar canzawar da kasar ta samu karkashin jagorancin JKS. Ana iya cewa, “Idan babu JKS, Sin ba za ta iya cimma irin wadannan nasarori ba.”

JKS wadda ta mai da muradun jama’a a gaban komai, an kafa ta ne don kawowa jama’a alheri, don haka tana hadin kai da jama’a don tinkarar wuhalhalu da dama. Abin da ya sa, kasa dake fama da koma baya wadda wasu kasashe masu mulkin mallaka a Turai su kan yiwa dariya, ta zama wata kasa dake da karfi matuka.

A ganinsa, akwai muhimman abubuwa guda uku, da ya kamata duk wata jam’iyya ta kasance tana da su, wato daidaito da adalci, da kuma samun goyon bayan jama’a. Maganar malam Gebi ta yi daidai da jigon taron na wannan karo, wato “Kawowa jama’a alheri: Nauyin dake kan wuyan jam’iyyu”. An iya nuna cewa, yanzu wannan ra’ayi ya samu amincewa daga bangarori daban-daban.

Ban da wannan kuma, a cewar malam Gebi, jam’iyya mai mulkin Najeriya wato APC, ko da yake ba ta fara hadin gwiwa da mu’ammala da JKS ba tukuna, amma tana koyon dabara da basirar JKS a fannin tsaro da kawar da kangin talauci, da kimiyya da kuma aikin gona da sauransu. A ganinsa, akwai abubuwa da yawa da ya kamata kasarsa ta koya, musamman ma yadda za a kawowa jama’a alheri. Ya ce, JKS tana mai da hankali matuka kan zaman rayuwa jama’a, tana maida muradun jama’a gaban komai. A gani na, shugabanni mafi yawa kamar malam Gebi na fahimtar cewa, alkibla da manufofin JKS, suna hada kan al’umma, ta yadda za a samu babban ci gaba.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba nuna cewa, ya kamata a kafa sabuwar dangantakar jam’iyyu, mai kunshe da gane bambanci da mutunta juna, da koyi da juna ta hanyar kara amincewa da juna, da tuntubar juna da kuma hadin kan juna, don bullo da sabuwar dangantakar jam’iyyun kasa da kasa, karkashin tushen sabuwar dangantakar kasa da kasa.

Haka ne, Sin tana bude kofarta ga waje, tana rike da ra’ayin tuntubar kasashe daban-daban. Kuma Sin tana fatan more dabaru da basirarta wajen samun ci gaba, tare da koyon wasu nagatattun manufofi, da dabarun samun ci gaba na sauran kasashe. JKS tana namijin kokarin tabbatar da aikin kawowa jama’a alheri, wanda hakan ya samu amincewa daga jama’a. Ana hadin kai don samun ci gaba tare. Wannan shi ne abun da JKS take son ta bayyanawa dukkanin fadin duniya, a fannin samun ci gaba mai dorewa, a yayin taron na wannan karo. (Amina Xu)