logo

HAUSA

Ya dace a ciyar da hulda tsakanin Sin da Turai gaba bisa tushen moriyar juna

2021-07-06 20:38:36 CRI

Ya dace a ciyar da hulda tsakanin Sin da Turai gaba bisa tushen moriyar juna_fororder_eu

Jiya Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, da kuma shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, sun yi taron koli ta kafar bidiyo a nan birnin Beijing, taron da ya kasance karo na biyu da shugabannin uku suka kira a cikin watanni uku da suka gabata.

Kasar Sin da kasashen Turai, suna taka muhimmiyar rawa a tsarin kasa da kasa, kuma babu sabani mai tsanani dake tsakanin sassan biyu, amma a cikin ‘yan kwanakin da suka wuce, wasu al’ummun kasashen Turai sun bi umurnin wasu ‘yan siyasar Amurka, kuma sun yi suka ga kasar Sin bisa fakewa da batutuwan dake shafar yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang dake kasar Sin, haka kuma sun dauki matakin hana aiwatar da yarjejeniyar zuba jari ta Sin da Turai, duk wadannan sun kawo cikas ga ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu.

Kan wannan batu, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, “Ya dace kasar Sin da kasashen Turai su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, bisa tushen martabar juna da yin hakuri da juna, ta yadda za su cimma burin ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba bisa tushen moriyar juna.”

Game da shawarar da Xi ya gabatar, shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun nuna amincewarsu, inda Merkel ta yi tsokaci da cewa, “Ina fatan za a kira taron ganawar shugabannin kawancen Turai wato EU da kasar Sin karo na 23 a kan lokaci, kuma ina fatan za a amince da yarjejeniyar zuba jari ta Turai da Sin a kan lokaci.”

A nasa bangare, Macron shi ma ya nuna goyon bayansa ga amincewar yarjejeniyar zuba jari ta Turai da Sin, kuma yana fatan hakan zai kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, wajen dakile sauyin yanayi da sauran batutuwan da suka fi jawo hankalinsu. (Jamila)