logo

HAUSA

Kayan Aro Baya Rufe Katara

2021-07-06 16:44:19 CRI

Kayan Aro Baya Rufe Katara_fororder_微信图片_20210706160550

Kayan Aro Baya Rufe Katara_fororder_微信图片_20210706160554

Kayan Aro Baya Rufe Katara_fororder_微信图片_20210706160556

Kayan Aro Baya Rufe Katara_fororder_微信图片_20210706160558

Daga Fa’iza Mustapha

Hausawa kan ce duk wanda ya bar gida, gida ya barshi! Duk da yadda alummomi daban daban a duniya suka yi watsi da aladunsu domin tafiya da zamani, da kuma irin ci gaban da Sin take samu a tsakanin kasashen duniya, sam alummarta ba su yi watsi da aladunsu ba. Wato dai, sun yi riko da shi , ba su yi aro kamar yadda wasu ke yi ba.  Ziyarata a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin ya fahimtar da ni abubuwa da dama, ciki har da yadda alummomi daban-daban suka dukufa wajen kiyaye aladunsu na gargajiya. Abun mamaki ne yadda wasu kafafen yada labaran yammacin duniya da ma kasashensu ke zargin kasar Sin da kokarin dakushe sauran kabilun kasar, inda suke ikirarin ta na kokarin raya kabilar Han da ta kasance mafi rinjaye a kasar. A baya, na dauka yan kabilar Uygur ne kadai a jihar Xinjiang, sai na sha mamakin tarar da Kabilu da dama kamar na Mongol da Kabilar Kazak da mafiya rinjayensu musulmai ne da kabilar Uzbek da Xibo da sauransu. A duk wuraren da na je, na kan tarar da duk wata suna ko alama da za a rubuta, akan rubuta su ne da harsuna daidaitccen Sinanci wato Mandarin da kuma harshen kabilar yankin. Misali, a Urumqi naga alamomi da harshen Uygur, a Bole, na ga ana rubutawa da harshen Mongol, yayin da a Yili ake rubutawa da harshen Kazak. Wannan manuniya ce cewa, lallai gwamnati na girmama aladun kabilu daban daban na kasar.

Baya ga haka, na ga yadda gwamnati ta kashe makudan kudi har sama da yuan miliyan dari uku wajen gina dakin nune-nunen wasanni da aladun gargajiya a yankin Yili.  Kuma an gina wannan daki ne da nufin raya aladun gargajiya na kabilu daban-daban na yankin. Wannan daki na da masu wasanni da suka kai 219 da suka fito daga kabilu daban-daban mazauna yankin Yili, lamarin da ke kara nuna yadda alummar kabilun yankin ke rayuwa cikin lumana karkashin inuwa daya tare kuma da raya aladunsu na gargajiya.

Misali na gaba shi ne, yadda aka kafa kasuwar da ake kira Bazaar a birnin Urumqi, wadda makasudinta shi ne, sayar da kayayyaki daban- daban na aladun gargajiya ga masu yawon shakatawa tare da gudanar da wasannin da raye-rayen gargajiya har ma da nuna irin abincinsu da ya fi shahara. A tunanina, duk gwamnatin da za ta ware wani yanki ko kudi don raya kananan kabilu, bata da burin dakushesu.

Har ila yau, an kebe wani wuri musammam domin nuna al’adun kabilar Xibo, inda ake nuna fasahar harbi da kori da baka da ta kasance fasahar da kabilar ta mallaka. Har ma da dakunan nune-nunen sanaoinsu, da yadda suke dafa nau’in abinsu.

Alummomin Jihar Xinjiang na amfani da irin niima da arzikin da suke da shi wajen samun kudin shiga da yayata aladunsu, ta hanyar jan hankalin masu yawon shakatawa daga ciki da wajen kasar Sin. Babu kabilar da ta yi watsi da aladu ko tarihinta. Baya ga haka gwamnati na tallafa masu wajen wannan sanaa. A zamana a kasar Sin, ban taba ganin wani Basinen da bai san asalinsa ko tarihi ko harshen kabilarsa ba. Har kullum kiran shugaban kasar shi ne kada a manta aladu yayin da ake kokarin neman ci gaba da samun wadata. Sannanan rayuwar alummar abu ne gwanin ban shaawa domin yadda suke zama cikin lumana da kwanciyar hankali, haka kuma akwai jituwa a tsakaninsu. Wannan kadai ya isa ya samarwa kasar ci gaban da take bukata. Bambancin aladu da kabila ko addini, abu ne dake kawata kasa domin yana bayyana irin kyawawan abubuwan da ta mallaka da asalin mutane daban daban,  haka kuma zaman jituwa a tsakaninsu shi zai kai ta ga samun ci gaba da wadata. (Fa’iza Mustapha)