logo

HAUSA

Kafofin watsa labaran Japan: Za a bude gasar wasannin Olympics ta Tokyo ba tare da ‘yan kallo ba

2021-07-06 10:47:17 CRI

Kafofin watsa labaran Japan: Za a bude gasar wasannin Olympics ta Tokyo ba tare da ‘yan kallo ba_fororder_222

Kafar watsa labaran Japan, mai suna Asahi Shimbun, ta bayyana cewa, gwamnatin Japan, tana daf da kammala shirye-shiryen da suka wajaba, na ganin an bude gasar wasannin Olympics a ranar 23 ga watan Yulin wannan shekara, ba tare da ‘yan kallo ba. Bugu da kari, wasu jami’an gwamnatin kasar, sun bayyana cewa, baya ga bikin bude gasar, za a bar ‘yan kallo su kalli wasu manya da kananan wasanni na gasar.

Rahotanni na cewa, galibin wasannin da ake gudanarwa ba tare da ‘yan kallo ba, sun hada da wasannin da ake gudanarwa bayan karfe 11 na dare, da wasannin da ake yi a filayen dake daukar ‘yan kallo sama da dubu biyar. Sai dai kuma, za a bar filayen da ba su kai wannan girman ba, su bar ‘yan kallo su shiga bisa wani sharadi.

Ana kuma saran, mambobin kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, da jami’an diflomasiya, daga kasashe daban-daban, da masu daukar nauyin shirya gasar, za su halarci bikin bude gasar. Wannan ya sa, wasu a cikin gwamnatin Japan, ke nuna damuwar cewa, wannan mataki na iya diga ayar tambaya daga kasashen ketare, inda suka bayar da shawarar cewa, ya kamata a rage yawan wadanda za su kalli gasar, zuwa a kalla daruruwan mutane.(Ibrahim)