Sunusi Abubakar: Ina kira ga matasan arewacin Najeriya su rungumi aikin noma
2021-07-06 16:05:43 CRI
Sunusi Abubakar, wani dan asalin jihar Bauchin tarayya Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a harkar noma a cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin ko kuma CAAS a takaice.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Sunusi Abubakar wanda ya zo China karo ilimi a shekara ta 2019, ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin, da bambancin ayyukan gonar da ake gudanarwa tsakanin kasashen biyu. Ya kuma ce, kasar Sin tana ci gaba sosai a fannin kimiyyar aikin gona, kuma tana da kayayyaki da na’urorin zamani da dama a wannan fanni, al’amarin da ya sa Najeriya da Sin ya dace su fadada hadin-gwiwa da mu’amala a wannan fanni.
A karshe, Sunusi ya kuma yi kira ga mutanen Najeriya, musamman matasan dake arewacin kasar, su tashi tsaye su rungumi aikin gona, da ake yiwa kirari da tushen arziki don bunkasa rayuwarsu. (Murtala Zhang)