logo

HAUSA

Ana gudanar da ayyukan gina tashar Lekki kamar yadda aka tsara

2021-07-05 14:56:20 CRI

Ana gudanar da ayyukan gina tashar Lekki kamar yadda aka tsara_fororder_2

Ya zuwa watan Yuni na bana, an yi nasarar kammala rabin aikin gina tashar jiragen ruwa ta Lekki dake gabashin birnin Lagos na kasar Nijeriya, wadda za ta kasance daya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa masu zurfi a yammacin nahiyar Afirka.

Dangane da wannan tashar jiragen ruwa, Maryam Yang na dauke da karin bayani…

An tsara aikin gina tashar jiragen ruwa ta Lekki bisa sakamakon da aka cimma a taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa na shawarar “Ziri daya da hanya daya” karo na biyu na shekarar 2019. Kamfanin CHEC na kasar Sin, da kamfanin Tolaram na kasar Singapore, da hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta kasar Nijeriya da kuma gwamnatin jihar Lagos ne, suke gudanar da aikin gina wannan tasha, kuma, gaba daya sun zuba jarin dallar Amurka miliyan 1044 kan aikin.

Bisa jadawalin da aka tsara, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2022, za a kammala kashin farko na aikin gina tashar jiragen ruwa ta Lekki, inda za a kebe wuraren tsayawar jiragen ruwa masu dauke da manyan sundukan daukar kaya guda biyu, kuma gaba daya, za a iya sauke manyan kwantenoni kimanin miliyan 1.2 ko wace shekara. Babban manajan sashen injiniya dake kula da shirin tashar Lekki na kamfanin CHEC Liu Chengjun ya bayyana cewa,“A halin yanzu, muna gudanar da ayyukan gina tashar jiragen ruwa, da kafa dandamali, da kuma habaka da zurfafa yankin ruwa da sauransu, gaba daya, an gama kaso 55% na aikin. Kuma, idan muka ci gaba da ayyukanmu bisa jadawalin da muka tsara, tabbas, za a kammala aikin baki daya bisa yarjejeniyar da muka kulla.”

Ana gudanar da ayyukan gina tashar Lekki kamar yadda aka tsara_fororder_1

Shugaban kamfanin tashar jiragen ruwa ta Lekki ta kasar Nijeriya Du Ruogang ya ce, tashar Lekki tana cikin yankin ciniki cikin ‘yanci na jihar Lagos, kuma tana kusa da yankin ciniki cikin ‘yancin na Lekki, da masana’antar sarrafa man fetur ta Dangote da masana’antun samar da takin zamani da sauransu, gina wannan tasha, zai taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin wurin, yana mai cewa,“Gina tashar jiragen ruwa ta Lekki, za ta taimaka matuka ga kasar Nijeriya wajen raya kasa, musamman ma, a fannin kara karfinta na safarar hajoji. A matsayinta na cibiyar sufurin hajoji, tashar Lekki tana da muhimmanci wajen karfafa musayar hajoji a tsakanin sassa daban daban, ta yadda za ta ba da gudummawar raya tattalin arzikin yankin bai daya, da inganta hadin gwiwar Sin da Nijeriya a fannin raya makamashi, da kuma habaka shirye-shiryen hadin gwiwar “ziri daya da hanya daya” kamar yadda ake fata.”

Da take tsokaci kan aikin gina tashar Lekki, shugabar sashen kula da hulda da jama’a Adesuwa Ladoja ta bayyana cewa, hakika, kasar Sin aminiyar kasar Nijeriya ce, tana kuma ba da taimako matuka ga kasar Nijeriya wajen gina babbar tashar jiragen ruwa, da layukan dogo da sauran ababen more rayuwa. Tana mai cewa,“Na shafe shekaru 10 ina aiki a shirin gina tashar jiragen ruwa ta Lekki, kuma, bisa nazarin da na yi, shawarar “ziri daya da hanya daya” shwara ce mai ma’ana sosai, domin za ta kawo mana babban ci gaba. Aikin gina tashar Lekki yana da matukar muhimmanci wajen raya sana’ar sufuri, zai hada mu da sauran kasashen duniya a fannin kasuwanci, baya ga karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Nijeirya da kasar Sin.”

Rahotanni na cewa, kamfanin CHEC ya zabi kamfanin zirga-zirgar jiragen ruwa na CMA-CGM na kasar Faransa a matsayin abokin huldarsa, domin kula da harkokin tashar Lekki yadda ya kamata. Sabo da a cewar kamfanin CHEC, kamfanin CMA-CGM yana da fasahohi masu kyau a fannin tafiyar da harkokin tashar jiragen ruwa. Kana, bisa jadawalin da aka tsara, ya zuwa karshen shekarar 2022, za a gama aikin gina tashar, sa’an nan, za a fara amfani da tashar Lekki a watan Maris na shekarar 2023 a hukumance. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)