logo

HAUSA

Ba zai yiwu a gurgunta hulda tsakanin JKS da al’ummun kasar Sin ba

2021-07-05 20:40:12 CRI

Ba zai yiwu a gurgunta hulda tsakanin JKS da al’ummun kasar Sin ba_fororder_jks

A yayin babban taron taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Xi Jinping ya sanar da cewa, ba zai yiwu a cimma yunkurin gurgunta huldar dake tsakanin JKS da al’ummun kasar Sin ba.

Idan an waiwayi tarihin kwazon jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a cikin shekaru 100 da suka gabata, cikin sauki za a fahimci matsayar da shugaban kolin JKS ya nuna.

Tun farkon kafuwarta, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi alkawarin cewa, ya zama wajibi a mayar da moriyar al’ummun kasar a gaban komai, kuma a cikin shekaru 100 da suka gabata, al’ummun Sinawa suna kokarin gina sabuwar kasar Sin karkashin jagorancin JKS, haka kuma suna kokarin gina kasa mai tsarin gurguzu, ta hanyar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare, a yanzu haka kuma sun sanar da cewa, sun cimma burin gina zamantakewar al’umma mai matsakaiciyar wadata, nan gaba kuma za su samu wadata tare, don haka cikin sauki ana iya lura cewa, babban burin JKS shi ne samar da wadata ga al’ummun kasar.

Rahoton bincike kan amincewa na shekarar 2020, wanda sanannen kamfanin ba da shawara wato Edelman ya fitar ya nuna cewa, amincewar da al’ummun kasar Sin suke nunawa gwamnatin kasarsu, ta kai kaso 95 bisa dari, alkaluman da ya kai matsayin koli a tsakanin daukacin kasashen da aka yi musu bincike. (Jamila)