logo

HAUSA

Abu mafi muhimamnci ga ci gaban JKS shi ne yaki da cin hanci da rashawa

2021-07-04 16:26:26 CRI

Abu mafi muhimamnci ga ci gaban JKS shi ne yaki da cin hanci da rashawa_fororder_JKS

A yayin babban taron taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS da aka gudanar a ranar 1 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar, Xi Jinping, ya bayyana cewa, duk da cewa, jam’iyyar JKS tana shan fama da matsaloli, amma ta samu ci gaba yadda ya kamata, har ma tana cike da kuzari, muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne, domin a ko da yaushe tana gudanar da al’amurranta bisa doka.

Idan an waiwayi kokarin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin take yi a cikin shekaru dari daya da suka gabata, an lura cewa, gyara kuskure cikin lokaci alama ce da ta bambanta JKS da sauran jam’iyyu daban daban, tun tuni wato a shekarar 1926, sai jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fitar da takardar yaki da cin hanci da rashawa ta farko a tarihi.

Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta samar sun nuna cewa, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, gaba daya adadin batutuwan shari’ar da hukumomin tabbatar da da’a da bin diddigi na kasar suka bincika ya kai miliyan 3 da dubu 805, kuma adadin mutanen da aka hukunta ya kai miliyan 4 da dubu 89. Kana tun lokacin fara aikin kama masu cin hanci da rashawa wadanda suka tsere zuwa kasashen waje a shekarar 2015, gaba daya adadin mutanen da aka tusa keyarsu zuwa nan gida kasar Sin daga kasashen ketare 120 ya kai sama da 9100, kuma adadin kudin da aka karba daga wajensu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 21.

Hakazalika wani rahoton binciken da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a karshen shekarar 2020 ya nuna cewa, al’ummun Sinawa kaso 95.8 bisa dari suna cike da imani kan aikin yaki da cin hanci da rashawa na JKS, adadin da ya karu da kaso 16.5 bisa dari idan an kwatanta da alkaluman da aka fitar a shekarar 2012.(Jamila)