logo

HAUSA

Ga yadda jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe ta wallafa labaru masu alaka da kasar Sin cikin shekaru 100 da suka gabata

2021-07-02 12:27:57 CRI

Daga shekarar 1921 zuwa ta 2021, tarihin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS ya kai tsawon shekaru 100. An kafa jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe a shekarar 1891, sakamakon haka, ta zama jarida mafi tsawon tarihi da aka fi sayar da ita a kasar Zimbabwe. A cikin shekaru 130 da suka gabata, yawan labaru masu alaka da kasar Sin da aka wallafa a jaridar ya yi ta karuwa, sannan sun fara ne daga labaru kadai, inda har suka kai matsayin rahotanni.

Ga yadda jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe ta wallafa labaru masu alaka da kasar Sin cikin shekaru 100 da suka gabata_fororder_210702-Sanusi Chen-rahoto-hoto1.JPG

A cikin watanni 3 da suka gabata, madam Tendai Manzvanzvike, shugabar cibiyar adana bayanai ta jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe ta taimakawa wakilanmu dake kasar Zimbabwe, nazartar labaru masu alaka da kasar Sin da aka wallafa a jaridar a cikin shekaru 100 da suka gabata. An gano cewa, a shekarar 1921, a kan samu kalmar “yunwa”, amma a shekarar 1949, an samu kalmar “sauyi”, sannan a shekarar 1971, kalmar “tashi tsaye”, zuwa yanzu kuma kalmar ita ce “karfi”. An gano cewa, wadannan kalmomi masu alaka da kasar Sin da suka bullo a jaridar sun bayyana yadda al’ummun Sinawa suka yi gwagwarmaya ba tare da kasala ba bisa jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS cikin shekaru 100 da suka gabata.

Tendai Manzvanzvike ta ce, a shekarar 1921, an yi amfani da kalmar “yunwa” a cikin rabin labaru da rahotanni 14 masu alaka da kasar Sin.

“A shekarar 1921, labaru masu alaka da kasar Sin da aka wallafa su a jaridar ba su da yawa. Amma idan an karanta wadannan rahotanni, za a iya gane cewa, kasar Sin tana cikin mawuyacin hali a wancan lokaci.”

Ga yadda jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe ta wallafa labaru masu alaka da kasar Sin cikin shekaru 100 da suka gabata_fororder_210702-Sanusi Chen-rahoto-hoto2.JPG

Ya zuwa shekarar 1949, muhimmiyar kalmar da a kan yi amfani da ita a lokacin da ake yada labaru masu alaka da kasar Sin ita ce “sauyi”. Labaru da rahotanni sun kunshi yadda rundunar soji dake karkashin jagorancin JKS take samun nasarori daya bayan daya, da kafuwar sabuwar kasar Sin da dai makamatansu. Tendai Manzvanzvike na ganin cewa, wannan sauyi ya bayyana cewa, nasarorin da JKS ta samu da kuma sabuwar kasar Sin sun jawo hankulan duk duniya sosai.

“Gwamnatin Rhodesia ta wancan lokaci da kasar Burtaniya mai mulkin mallakar Rhodesia dukkansu sun mai da hankulansu kan yanayin da ake ciki a kasar Sin. A hakika dai, ba kawai labaru masu alaka da kasar Sin ake wallafawa a shafin farko na jaridar ba, har ma a kan wallafa wasu rahotanni domin zurfafa nazarin al’amuran da suka faru a kasar Sin. Wannan ya bayyana cewa, kasar Sin na da muhimmanci sosai a duk duniya a wancan lokaci.”

Bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin, kalmar “tashi tsaye” ta kan fito a cikin rahotanni masu alaka da kasar Sin a kan wasu jaridun kasashen Afirka. A ran 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da wata shawarar da aka gabatarwa babban taron MDD, inda aka tsai da kudurin mayar wa jamhuriyar jama’ar Sin dukkan halaltattun ikonta a MDD. Jaridar “the Rhodesia Herald” ta wallafa wani dogon rahoto game da wannan muhimmin al’amari, inda aka nuna cewa, bisa jagorancin JKS, kasar Sin, wato wata kasa mai rauni kuma mai fama da yunwa a da, ta zama wata muhimmiyar kasa wadda take iya kawo tasiri ga sauran kasashen duniya, masana’antun kasar Sin ma sun samu ci gaba cikin sauri.

A cikin ’yan shekarun baya, jaridar “the Herald” ta kasar Zimbabwe ta fi mai da hankali kan yadda kasar Sin take samun dawaumammen ci gaban tattalin arziki, da yadda hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka take karfafuwa. Madam Tendai Manzvanzvike ta ce, yanzu “karfi” da “bunkasuwa” da “hadin gwiwa” sun zama muhimman kalmomin da su kan bullo a cikin rahotanni masu alaka da kasar Sin.

Ga yadda jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe ta wallafa labaru masu alaka da kasar Sin cikin shekaru 100 da suka gabata_fororder_210702-Sanusi Chen-rahoto-hoto3

“Yanzu mun fi mai da hankali kan yadda kasar Sin take kokarin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci a cikin rahotanninmu. Sannan muna mai da hankali kan yadda sauran kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka suke cin gajiyar ci gaban da kasar Sin ta samu. Mun wallafa rahotanni masu alaka da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ da yawa. Bisa jagorancin JKS, kasar Sin, wato wata kasa mai rauni kuma mai fama da yunwa a da, ta zama wata kasa mai karfi sosai a yanzu. Ya kamata mu yi koyi da kasar Sin.”

Madam Tendai Manzvanzvike ta taba ziyartar kasar Sin har sau biyu. Tana fatan karin ’yan Zimbabwe za su iya kawo wa kasar Sin ziyara, domin ganewa idanunsu yadda kasar Sin take samun ci gaba, ta yadda za a iya koyon fasahohin neman ci gaba da kasar Sin take da su domin bunkasa wata kyakkyawar kasar Zimbabwe. (Sanusi Chen)