Fitilar mai mai jan karfe irin na ”Good Luck”
2021-07-02 10:23:37 cri
Masu binciken kayan tarihi na Isra’ila sun gano wani fitilar mai mai jan karfe irin na ”Good Luck”, wanda aka gano a lokacin da aka binciko kayan tarihi a kan hanyar Hajji a wajen tsohon birnin Kudus. A wajen karni na 1 Miladiyya, magina sun binne fitilun mai jan karfe wanda ke alamta sa'a da wadata a cikin ginin don addu'a ga ginin da masu da shi. (Bilkisu)