logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin murnar cikar jam’iyyar kwaminis shekaru 100 da kafuwa

2021-07-01 21:00:19 CRI

Shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin murnar cikar jam’iyyar kwaminis shekaru 100 da kafuwa_fororder_1127614524_16251034744441n

Yau Alhamis ne aka yi gagarumin bikin murnar cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko kuma JKS a takaice a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, bikin da ya samu halartar mutane sama da dubu 70 daga bangarori daban-daban na kasar. Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis, wanda kuma shi ne shugaban kasar, kana shugaban rundunar sojan kasar, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi.

Shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin ta cimma burin raya al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni, abun da ya sa ta warware matsalar kangin talauci, kuma tana ci gaba da namijin kokarin cimma wani buri, wato raya kasar Sin mai karfi ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkanin fannoni.

A cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya ce, kafa jam’iyyar kwaminis, wani babban al’amari ne, wanda ya sauya alkibla da makomar jama’ar kasar baki daya. Tun kafuwar ta zuwa yanzu, jam’iyyar tana maida aikin samar da alheri ga jama’ar kasar da farfado da al’umma a matsayin burin da take kokarin cimmawa, inda ya ce:

“A cikin shekaru 100, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta hada kan al’ummomin kasar don yin gwagwarmaya da sadaukarwa gami da kirkiro sabbin abubuwa, kuma burinsu daya ne, wato samun farfadowar al’ummar kasar.”

Shugaba Xi ya ce, a shekaru 100 da suka wuce, jam’iyyar kwaminis ta jagoranci al’ummar kasar Sin don nuna jaruntaka da jajircewa wajen aiki. Kuma hanyoyin da aka lalubo, da sana’o’in da aka kirkiro gami da manyan nasarorin da aka cimma, ko shakka babu za’a rubuta su cikin tarihin ci gaban al’ummar kasar Sin da tarihin ci gaban wayin kan daukacin al’umma.

Shugaba Xi ya ce:

“Dukkan nasarorin da muka samu cikin shekaru 100, sakamako ne na aiki tukuru da ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis da jama’ar kasar da ma daukacin al’ummomin kasar suka yi cikin hadin-gwiwa. Wasu muhimman jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da Mao Zedong, da Deng Xiaoping, da Jiang Zemin, da Hu Jintao, sun bayar da babbar gudummawa ga aikin farfado da al’ummar kasar Sin, kuma ya kamata mu girmama su.”

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya zama dole mu aiwatar da wasu muhimman manufofi, ciki har da “Tsarin kasa daya amma tsarin mulki biyu”, da “jama’ar yankin Hong Kong su mulki yankin”, su ma “jama’ar yankin Macau su mulki yankin”, kuma a ba su babban ikon cin gashin kansu, a kokari na tabbatar da dauwamammen ci gaba da kwanciyar hankali a Hong Kong da Macau.

Shugaba Xi ya ce: “Ya kamata a tsaya ga manufar kasar Sin daya tilo a duniya, da matsayar da aka cimma tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan a shekara ta 1992, da kokarin dinke kasa baki daya ta hanyar lumana. Kamata ya yi daukacin al’ummar kasar Sin, ciki har da na babban yankin kasar da na Taiwan, dukkansu su zama tsintsiya madaurinki daya, da yakar duk wani makircin da aka kulla na neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin, da kirkiro makoma mai haske ga al’ummomin kasar.”

Shugaba Xi ya jaddada cewa, a shekaru 100 da suka gabata, ayyukan da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi, sun gamsar da al’umma gami da tarihi. A halin yanzu, jam’iyyar tana shugabantar al’ummar kasar wajen kama hanyar neman cimma babban buri na daban, wato raya kasar Sin mai karfi ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkanin fannoni nan da shekara ta 2049.

A karshe, shugaba Xi ya bayyana cewa:

“Abokai, aminai! Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana bakin kokarinta wajen farfado da al’ummar kasar. Idan mun yi waiwaye adon tafiya tare da hangen nan gaba, za mu gano cewa, bisa jagorancin jam’iyyar kwaminis, da hadin-gwiwar al’ummomi daban-daban, babu shakka za mu cimma burin raya kasar Sin mai karfi ta zamani mai bin tsarin gurguzu daga dukkanin fannoni.” (Murtala Zhang)