Du Ziwei: Ina fatan za a yada wasan filfilo na gargajiya na Sin a dukkan duniya baki daya
2021-07-01 15:05:49 CRI
Wasan filfilo, wasa ne na gargajiya na kasar Sin. A kan ce, wasan filfilo, wasan yara ne. Filfilo yana da tarihin fiye da shekaru dubu biyu. Sinawa su kan yi zane-zane masu alamar fatan alheri kan filfilo. Siffar filfilo tana yin kama da dabbobi ko tsuntsaye. A kan yi amfani da takarda ko siliki wajen kera filfilo.
Du Ziwei, dalibi ne a jami’ar wasannin motsa jiki ta Shanghai, wanda ya yi nazari kan bunkasuwar wasan gargajiya na kasar Sin, kamar su wasan rawar dragon da zaki, da wasan filfilo, da wasan kayan Kongzhu, da wasan tseren kwale-kwale wato dragon boat da sauransu. Ya kuma ce dalilin da ya sa jami’arsa ta kafa irin wannan sashe shi ne, samar da dama ga matasa, ta koyon wadannan wasannin gargajiya na Sin, da kuma fahimtar al’adun gargajiya na Sin ta wasannin.
A farkon shekarar 2019, ya shiga jami’ar wasannin motsa jiki ta Shanghai don neman samun digiri na biyu, a lokacin, ya fara koyon ilmin wasan filfilo a jami’a. Ya ce, kafin ya shiga jami’ar, ya iya wasan filfilo kamar sauran mutanen Sin. Lokacin da ya fara koyon wasan a jami’ar, ilminsa a wasan ya karu, kana kuma ya fara yin nazari kan wasan. Ya ce, akwai bambanci sosai a tsakanin yadda ake yin wasan a yau da kullum da kuma a jami’ar. Ya ce,“A yau da kullum, mutane su kan sayi filfilo a kasuwa, da yin wasan filfilo a waje a lokacin kadawar iska. Inji ne ya kera irin wannan filfilo, kuma akwai sauki yin wasa da irin wannan filfilo. Amma yayin da muke koyon wasan a jami’ar, ba ma kawai mun koyi yadda ake yin wasan ba ne, har ma mun koyi yadda aka kera filfilo. Mun koyi fasahohin gargajiya na kera filfilo, da yin zane-zane kan filfilo, da hade da takarda da sanda don kera filfilo, da kuma sa filfilo a cikin sama tare da iska. Don haka, ilmin da muke koya ba koyon yadda ake yin wasan kawai ba ne, muna ma koyon al’adun wasan, da kuma tunanin masu fasahohin kera filfilo.”
Kana ya ce, lokacin da yake yin zane-zane kan filfilo da kera filfilo, hankalinsa yana kwanciya. Tsofaffi ne akan ga yawanci suna yin wasan filfilo. Tsofaffi suna iya tabbatar da lafiyar jikinsu ta wasan.
Du Ziwei ya ce, a halin yanzu, yawancin mutane suna aiki ne a kujeru da tebur, kansu yana sunkuye a tsawon lokaci. Don haka, su kan samu matsalar lafiya a kafada da wuya. Idan mutane suke yi wasan filfilo, hakan na sa su daga kai da kallon filfilo dake cikin sama, don haka, za su iya motsa kafada da wuyarsu, da kuma warware matsalar lafiyar jikinsu ta wasan.
Du Ziwei ya bayyana cewa, da farko dai ya koyi wasan rawar dragon a jami’a, ya zabi wannan wasa domin yana sha’awar wasan, ya yi tsammani cewa, wasan ya yi kyau, da zai burge masu kallo sosai. Ya ce, irin wannan wasa wasan gargajiya ne na kasar Sin, kana za a fahimci al’adun wasan, da sauran al’adun gargajiya da tunanin Sin ta wasan. Daga baya, ya zabi koyon wasan filfilo da kansa, ya ce wasan filfilo ya yi kama da wasan rawar dargon, dukkansu wasanni ne na gargajiyar kasar Sin. Ya ce,“Wadannan wasannin gargajiya na kasar Sin dukkansu suna da tarihi na fiye da shekaru dubu biyu a kasar Sin. A matsayina na matashin kasar Sin, na zabi koyon wasannin motsa jiki, don me ba za a zabi wasannin gargajiya na Sin wadanda aka gaje su cikin dogon tarihi ba?”
Du Ziwei ya samu lambobin yabo da dama kan wasannin gargajiya na kasar Sin, ciki har da zakara na wasan rawar dragon da zaki na kasar Sin. Ya ce, har zuwa yanzu, babu gasar wasan filfilo a kasar Sin, sai dai yana yin wasan filfilo a fili kamar gwada fasahohi a gaban jama’a. Ya ce, ana bukatar fasahohi masu kwarewa, wajen yin wasan filfilo mai siffar dragon, ban da daga filfilon dragon a cikin sama, ya kamata masu yin wasan su nuna girmamawa ga dragon a cikin zuciyar su. Idan ba a tada filfilon dragon a cikin sama yadda ya kamata ba, filfilon zai lalace. Don haka, kwararrun wasan ne suke yin wasan filfilon dragon, su matasa suna bada taimako ne kawai.
Du Ziwei ya ce, iyayensa sun nuna goyon baya gare shi, wajen koyon wasannin gargajiya na Sin. Ya ce, yawan shekarun iyayensa ya zarce 50, su ma suna son wasannin gargajiya na kasar Sin.
A kan ce, yara sune manyan gobe. Du Ziwei ya ce, ana bukatar yara da matasa su ci gaba da yada wasannin gargajiya na kasar Sin. Don haka, yayin da yake yin kokarin yada wasannin gargajiya na kasar Sin, ya kan koyar da yara fasahohin wasannin. A cikin jami’arsa, tsoffin dalibai su kan koyar da fasahohin wasannin ga sabbin dalibai. Ta hakan, ake ci gaba da gadar wasannin gargajiya daya bayan daya.
Liu Yihua, sabuwar daliba ce mai neman digiri na biyu, a jami’ar wasannin motsa jiki ta Shanghai. Ta koyi fasahohin wasu wasannin gargajiya na kasar Sin, kamar wasan kayan Kongzhu daga tsoffin daliban ajinsu ciki har da Du Ziwei. Tana kuma ganin cewa, akwai alakar dake tsakanin wasannin zamani da wasannin gargajiya. Ta ce, koda yake ta yi wasannin zamani da farko, amma babu cikas game da ci gaba da koyon wasannin gargajiya. Bayan da ta fara koyon wasannin gargajiya, ta gano akwai ban sha’awa sosai. A nan gaba, za ta ci gaba da yin kokarin koyon fasahohin wasannin gargajiya na Sin, kana da yada su a cikin kasar Sin, ta hanyar zama malama a makaranta. Ta ce,“Bayan da na gama karatu a jami’ar, zan bada darussan wasannin motsa jiki a makaranta. A halin yanzu, akwai makarantun firamare na kasar Sin da dama dake bada darussan koyar da wasannin gargajiya na kasar Sin, kamar su wasan filfilo, wasan kayan Kongzhu da sauransu, kana za a koyar da yara yadda ake kera filfilo. Don haka, a gani na, akwai amfani ga koyon wasannin gargajiya na Sin, da samun kyakkyawar damar yada su a tsakanin yara.”
Bayan da dalibai masu koyon wasannin gargajiya a jami’ar suka samu digiri na farko, idan sun ci gaba da yin karatu don neman samun digiri na biyu, to ya kamata su kara yin nazari mai zurfi kan wasannin, kamar yadda ake tsara shirye-shiryen gwada wasannin gargajiya, da yadda ake kera kayayyakin wasannin gargajiya, da yadda ake yada wasannin gargajiya da sauransu, ba wai koyon fasahohin wasannin kawai ba.
Game da burinsa, Du Ziwei ya ce, zai ci gaba da koyon fasahohin wasannin gargajiya na kasar Sin, da yin kokarin bunkasa wasannin a cikin kasar Sin, har ma da yada su a kasashen waje. Du Ziwei ya bayyana cewa,“Dukkansu su wasannin gargajiya na kasarmu ta Sin ne, ina fatan za su kara samun karbuwa a cikin kasar Sin, har ma a iya yada su a sauran sassan duniya baki daya.”
Du Ziwei ya kara da cewa, ya zuwa yanzu akwai gasannin wasan gargajiya na kasar Sin da aka gudanar a kasashe daban daban na duniya, wannan ya sa kaimi ga yada wasannin gargajiya na Sin a sassan daban daban na duniya. Yana kuma fatan a nan gaba, ba ma kawai Sinawa ne za su rika son yin wasannin gargajiya na kasar Sin ba, har da ma al’ummun sauran kasashen duniya, za su nuna sha’awa da yin wasannin gargajiya na kasar Sin. (Zainab Zhang)