logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu gaggaruman nasarori a fannin gudanar da harkokin kasar, in ji Martin Jacques

2021-06-30 14:41:02 CRI

Kasar Sin ta samu gaggaruman nasarori a fannin gudanar da harkokin kasar, in ji Martin Jacques_fororder___172.100.100.3_temp_9500031_1_9500031_1_1_c22ea703-eea8-4699-804f-180831532ae6

A yayin da jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin ke dab da cika shekaru 100 da kafuwa, babban manazarci a jami’ar Cambridge ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu gaggaruman nasarori ta fannin gudanar da harkokin kasar, ya kuma yi kira ga kasa da kasa da su habaka hadin gwiwarsu. Wakiliyarmu Lubabatu na tare da karin haske.

A yayin zantawarmu tare da Martin Jacques, mashahurin shehun malami dan kasar Burtaniya, ya ce, idan an waiwayi shekaru 100 da suka wuce, ban da yake-yaken duniya guda biyu, kuma yadda aka kammala sabon salon juyin juya halin dimokaradiyya a kasar Sin, da ma kawo karshen mulkin mallaka a duniya, sun kasance muhimman al’amuran da ke haifar da babban tasiri ga duniya.

A yayin da ya tabo magana a kan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a tarihi, Prof. Martin Jacques yana ganin cewa, dalilin da ya sa hakan ya faru shi ne, kasar ta Sin tana bin hanyarta wajen bunkasa tsarin zaman al’ummarta, wanda ya sa ta samu gaggarumar nasara ta fannin gudanar da harkokin kasar. Yana mai cewa,“Yadda kasar Sin take bin hanyarta wajen bunkasa tsarin al’umma, ya sa ta samu gaggarumar nasara ta fannin gudanar da harkokinta, ya kuma kawo manyan sauye-sauye ga zaman al’ummar kasar, wanda ya sa kasar da ke da kaso 1/5 na al’ummar duniya, ta gyara irin yanayin da ta samu kanta a ciki na fama da talauci da koma baya a cikin wani gajeren lokaci.”

Baya ga haka, Prof. Martin Jacques ya kuma yaba da yadda kasar Sin ke goyon bayan cudanyar kasa da kasa, da ma hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakaninsu, da manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya da shugabannin kasar Sin suka gabatar. Ya ce,“A ganina, kasar Sin tana kallon rawar da take takawa a duniya, a matsayin bunkasa huldar da ke tsakaninta da kasashen duniya, wato tana yin komai ne domin amfanar kanta tare kuma da ‘yan Adam baki daya. Musamman ma bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare gyare a gida, da ma bude kofarta ga kasashen ketare. Alkiblar da take bi ita ce dora muhimmanci a kan bunkasa huldarta da sauran kasashen duniya, wato ke nan alkiblar da kasar ke bi ta yi daidai da ra’ayin cudanyar kasa da kasa, wanda ainihin ma’anarsa ita ce cin moriyar juna.”

A matsayinsa na sanannen masani a fadin duniya, Prof. Martin Jacques ya kuma yi nuni da cewa, akwai matsala ga tsarin jari-hujja na kasashen yammacin duniya. Ya ce,“A ganina, kasashen yammacin duniya na fuskantar matsala. A kalla daga farkon shekarun 1980, musamman ma bayan aukuwar rikicin hada-hadar kudi a shekarar 2008, kasashen yamma sun kasa daga matsayin rayuwar al’ummarsu, abin da a zahiri ya faru a kasar Amurka. Albashin da ake samu a kasar a yanzu bai kai na shekarar 2007 ba. Yanzu kimanin shekaru 14 a jere ana fuskantar irin wannan hali. A ganina, tabbas akwai babbar matsala ga tsarin jari-hujja da kasashen yammacin duniya ke bi.”

Har wa yau, shehun malamin ya jaddada cewa, kasashen yamma ba za su iya ci gaba da tilasta wa kasashe masu tasowa su mika wuyansu, kuma su yi abubuwan kamar yadda suke fata ba, ta hanyar tsoma baki cikin harkokinsu na siyasa, da daukar matakan soja kamar yadda suka saba.

A game da makomar duniya, Prof. Martin Jacques ya ce, kasashen duniya na bukatar kara habaka hadin gwiwa a tsakaninsu. Ya  ce,“Makomar kasashen duniya daya ce. Dunkulewar kasashen duniya a zahiri dai tana da muhimmanci, sai dai yanzu ta tsaya, har ma muna iya cewa ta dan koma baya. Amma idan mun yi hangen nesa, ina ganin ta zama abin da ba wanda zai iya hana ta wakana. Kasashen duniya na bukatar habaka hadin gwiwarsu a karin fannoni. Idan mun kasa yin hadin gwiwa, lallai ba za mu kai ga tabbatar da kyakkyawar makoma ta ‘yan Adam ba”.  (Lubabatu)