logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Samu Wadata Karkashin Jam’iyyar Kwaminis

2021-06-30 19:04:53 CRI

Kasar Sin Ta Samu Wadata Karkashin Jam’iyyar Kwaminis_fororder_0630-1

Yayin da al’ummar Sinawa a kasar Sin, ke shirye-shirye murnar cikar JKS shekaru 100 da kafuwa, jam’iyyar da ta jagorancin kasar ga cimma nasarorin da suka ba fito da sunanta a duniya baki daya, wasu kafofin watsa labarai a sassan duniya ciki har na yammacin kasashen duniya, sun nuna yabo ga Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, game da irin gagarumar rawar da ta taka, wajen kawar da talauci a kasar Sin, da kuma samun farfadowar kasa baki daya.

Wasu daga cikin irin wadannan sharhuna da jaridun suka wallafa, sun hada da mai taken “Dabarar JKS ta samun ci gaba”. Sharhin ya ci gaba da bayyana cewa, a duk fadin duniya, babu wata jam’iyya da ta tsira bayan da ta sha matukar wahala iri-iri, sa’an nan ta cimma nasarar raya kasarta zuwa kasa mai karfin ci gaban tattalin arziki har ta kai matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kamar JKS.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a, game da karbuwar JKS tsakanin al’ummar Sinawa ta nuna cewa, JKS ta samu amincewar jama’ar kasar Sin, ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen kara tasirin kasar Sin a harkokin kasashen duniya. Yanzu haka, kasar Sin ce ke kan gaba a fannonin dakile matsalolin sauyin yanayi, da neman farfadowar kasa bayan annobar COVID-19, da kuma kawar da talauci a duk duniya, inganta rayuwar al’ummar Sinawa, duk wadannan an cimma su ne karkashin jagorancin JKS.

A karkashin jagorancin JKS, kasar Sin ta shigo da tsarin tattalin arzikin kasuwanni a cikin shirinta na yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, ta kuma kafa tsarin tattalin arzikinta na kasuwanci mai tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sim, matakin da ya kafa wata sabuwar hanyar samun bunkasuwa cikin sauki ga kasar Sin.

Kyan alkawari aka ce cikawa, JKS ta cika alkawuran da ta dauka, misali yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kawar da kangin talauci, ta ingiza tsarin ba da jinya ga manoma, bisa hadin kan gwamnati da kamfanoni inshora da sauransu.

Masu fashin baki na cewa, Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, jam’iyyar da ta fara da mambobi kalilan, har ta kasance jam’iyyar mafi girma da karfi a duniya, ta dauki nauyin raya kasa, a lokacin da jama’ar kasar suke cikin mawuyacin hali, ta kuma zabi wata hanya mai dacewa da kasar Sin wajen neman bunkasuwa, lamarin da ya tabbatar da yanayin zaman karko, da samun wadata, da kuma hadin gwiwar al’ummomin kasar Sin.

Duk wanda ya kalli gagarumar rawa da nasarorin da kasar Sin ta cimma, wasu daga cikinsu ma, sun kasance na ban-al’ajabi da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, ana da imani da ma tabbaci cewa, kasar Sin za ta kara cimma nasarori karkashin jagorancin JKS. (Ibrahim Yaya)