logo

HAUSA

Yang Mei, wadda ta yi fama da talauci a da, amma mai jagorantar samun wadata a yau

2021-06-30 09:54:27 cri

Yang Mei, shugabar masana'antar saka tufafi ta Xingmei Hongyang da ke garin Kaili na lardin Guizhou, a da ta kasance mai fama da talauci, wadda ta yi zaman rayuwarta ta dogaro da taimakon gwamnati, amma yanzu ta zama mai jagorancin dabarun sada mutane da arziki tare, sakamakon ci gajiyar manufar kaura zuwa sauran wurare, domin kawar da talauci, da ma sauran manufofin gwamnati na ba da tallafi a fannin samar da guraban ayyukan yi.

Yang Mei, wadda ta yi fama da talauci a da, amma mai jagorantar samun wadata a yau_fororder_杨美1.JPG

Garin Yang Mei yana a kauyen Kaishao na garin Kaitang dake birnin Kaili. Wannan kauyen na kabilar Miao yana can cikin duwatsu, kuma ba ya samun ci gaba sosai, don haka, mazauna wurin da yawa sun taba neman aiki a waje domin kyautata zaman rayuwarsu.

A lokacin da Yang Mei take makarantar sakandare, mahaifinta ya kamu da rashin lafiya, hakan ya sa suka yi fama da talauci, har ta daina zuwa makaranta. Bayan ta yi aure, ita da mijinta sun tafi aiki a sauran wurare. A shekarar 2008, Yang Mei ta haifi danta na farko, amma ita da mijinta suna aiki a waje duk tsawon shekara, babu dabara sai iyayen mijinta ne suka kula da danta. Lokacin da danta ya cika shekaru uku, Yang Mei da mijinta sun koma gida daga waje don murnar bikin bazara. Yayin da suke cin abinci, danta ya taba kan kakansa da tuffa, a sa’i daya kuma ya kira sunan kakansa kai tsaye. Da ganin haka, Yang Mei ta yi bakin ciki kwarai, kuma ta zargi kanta kwarai da gaske saboda rashin bai wa danta kulawa da kuma ilimi.

A shekarar 2010, domin kara kulawa da iyalinta, Yang Mei ta koma birnin Kaili, kuma ta yi rayuwa ta hanyar yin kananan kasuwanci. A lokacin kuma, an soma inganta ayyukan kaura zuwa wurare daban-daban don kawar da talauci a birnin. A shekarar 2016, a matsayinsa na daya daga cikin rukunin farko na makaurata na unguwar Shangmashi dake birnin Kaili, iyalin Yang Mei ya kaura zuwa sabon gida mai murabba'in mita 90, wanda gwamnatin wurin ta bayar kyauta.

Yang Mei, wadda ta yi fama da talauci a da, amma mai jagorantar samun wadata a yau_fororder_杨美3.JPG

Domin magance matsalar yin rayuwa bayan kaura, Ofishin Rage Talauci na birnin ya shirya nau'o'in horas daban daban don samun aikin yi ga makaurata. Mahalarta horon ba kawai za su iya koyon fasaha ba ne, har ma za su sami tallafin kudi na samun horo a ko wace rana.

Yang Mei ta halarci kwasa-kwasai na koyon fasahar dinkin tufafi. Bayan karatun na tsawon watanni uku, sai ta kware kan yin tsare-tsare da gyaran keken dinki.

Bayan ta kammala karatu, Yang Mei tana da ra'ayin raya sana'arta, kuma ta gaya wa Zhang Rong, sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na Ofishin rage talauci kan ra'ayin ta na bude wani dakin dinki tufafi, ta yi fatan samun goyon baya daga wajensa. Zhang Rong ya nuna yabo sosai kan tunanin Yang Mei na raya sana’a da kanta, kuma ya karfafa mata gwiwa don bude wani kamfanin kawar da talauci, hakan zai ba da dama ta iya jagorantar karin makaurata su samu arziki. Ya kuma bayyana cewa, Ofishin rage talauci zai saya mata wurin gina kamfanin, da na’urorin dake bukata. Zhang Rong ya amince da kwazon aikin Yang Mei, don haka ta karfafa mata gwiwar kafa cibiyar yaki da fatara, don taimakawa karin mutane dake rabuwa da muhallin su samun damammakin arziki. Ofishin yaki da fatara a nasa bangare, shi ne zai samar mata da wuri da kuma kayayyakin aiki da take bukata.

A shekarar 2018, kamfanin Yang Mei, wanda ke da ginin masana'anta mai fadin sama da murabba'in mita 300, da kuma kekunan dinki sama da 10, ta soma aiki a hukumance.

Yang Mei, wadda ta yi fama da talauci a da, amma mai jagorantar samun wadata a yau_fororder_杨美2.JPG

Lokacin da ta fara kasuwancin ta, Yang Mei ta kasance shugaba ce kuma ma'aikaciya, kuma ta kasance mai tsara kayayyaki kuma mai sayarwa, sannan kuma ita ce ke da alhakin kula da injina, tana yin komai da kanta.

Ofishin kawar da talauci ko da yaushe yana kokarin biyan bukatunta, yana ba ta taimako don fadada masana'anta, da sayen kayan aiki, da samun rancen kudi daga banki.

Bisa goyon baya daga gwamnati da kuma kokarin da take yi, kamfanin dinki tufafi ta Yangmei yanzu ya fadada zuwa fiye da murabba'in mita 2000, tare da ma'aikata sama da 100, matsakaicin kudin shiga na kowane ma'aikaci ya kai yuan 2500 a ko wane wata. Ba wai kawai kamfanin yana samar da tuffafin makaranta, kayan kwalliya da tufafin kabilu daban daban ba ne, har ma akwai kayayyakin sake-sake da aka yi da hannu kuma aka sayar da su har zuwa wasu manyan biranen kasar kamar su Beijing, Shanghai, Guangzhou da dai sauransu.

“Ko da yaushe a kasance da zuciya mai godiya kuma ko da yaushe a yi tunanin mutanen da suka ba mu taimako”. Yang Mei, wadda aikinta ke kan hanya madaidaiciya, yanzu tana kara tunanin yadda za ta ba da gudummawa ga al'umma.

Yang Mei ta ce, tabbas za ta tafiyar da masana'antar dinki tufafi yadda ya kamata, kuma tana fatan 'yan uwanta mata da suke fuskantar matsaloli daban daban kamar yadda ta yi a da, za su iya yin aiki a kamfaninta, hakan ba wai kawai zai sa su iya kula da iyalinsu ba ne, har ma za su iya samun kudin shiga mai kyau, ta yadda za a iya samu arziki tare.