logo

HAUSA

Nasarorin da jam’iyya Kwaminis ta kasar Sin ta cimma cikin shekaru 100 cif da kafuwa

2021-06-30 09:11:03 CRI

A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021 ne, JKS take cika shekaru 100 da kafuwa. Jami’iyyar da ta fara da mambobi kalilan, yanzu ta kasance jam’iyya mafi yawan mambobi da girma a duniya. Haka kuma JKS ta zama jam’iyyar da ta yi nasarar jagorantar al’ummar Sinawa wajen tsame baki dayan jama’arta daga kangin talauci, cikin wani wa’adi da ya baiwa duniya mamaki matuka.

Nasarorin da jam’iyya Kwaminis ta kasar Sin ta cimma cikin shekaru 100 cif da kafuwa_fororder_20210630世界21024-hoto2

Sai dai a yayin da wasu kasashen duniya ke taya kasar Sin murnar cikar wannan babbar jam’iyya shekaru 100 da kafuwa, da ma tarin nasaroin da kasar ta cimma karkashin jagorancinta, wasu kasashen yamma da ’yan kanzaginsu, na nuna adawa da manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma, har ma suke neman bata sunanta da yada karaikayi kan wasu manufofi da take dauka a wasu yankunanta, don neman cimma burinsu na siyasa.

Kadan daga cikin irin wadannan nasarori, sun hada da fitar da al’umma daga kangin talauci, gina al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, dakile yaduwar annobar COVID-19 da samar da alluran riga kafin cutar. Sauran sun hada da nasarar a fannin binciken sararin samaniya, fannin fasahohin kimiya da na kirkire-kirkire, da sauransu.

Nasarorin da jam’iyya Kwaminis ta kasar Sin ta cimma cikin shekaru 100 cif da kafuwa_fororder_20210630世界21024-hoto3

Har kullum kasar Sin tana kira a martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa da ya dace da yanayin da suke ciki, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, da martaba ka’idar alakar kasa da kasa, ta yadda za a gina al’ummma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama..

A cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta shaida ta hanyar daukar hakikanin matakai cewa, ita jam’iyya ce mai kishin zaman lafiya da neman ci gaba, abin da masu fashin baki ke cewa, JKS za ta kara jagorantar al’ummar Sinawa, wajen cimma tarin nasarori na ban-al’ajabi a duniya a nan gaba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)