logo

HAUSA

Jama’a Suna Kaunar Jam’iyyar Dake Iya Kawo Musu Alheri

2021-06-30 18:16:50 CRI

 

Jama’a Suna Kaunar Jam’iyyar Dake Iya Kawo Musu Alheri_fororder_8E0A6BD9-E71A-43D7-BBE1-5AE864ED1CEB

Daga Amina Xu
Daga shekarar 2016 zuwa 2018, na yi aiki a Najeriya, kuma na taba ziyartar kasashen Afrika da dama, inda wasu ‘yan Afrika da suka gane cewa ni ‘yar kasar Sin ce, su kan ambaci “Chairman Mao”, wato shugaban farko na jamhuriyyar jama’ar kasar Sin. Sabo da marigayi Mao Tsedong ya jagoranci jama’ar Sin wajen kawo karshen mulkin mulaka’u da mulkin mallaka a kasar, baya ga kuma marigayi Mao Tsedong da sauran tsoffin shugabannin Afrika sun hada kansu wajen bude wani sabon babin dangantakar bangarorin biyu, tare da samun ‘yancin kan kasar da farfadowar al’umma. Amma ina dalilin da ya sa jama’a suka kuduri aniyar bin marigayi Mao wajen yin juyin juya hali, kuma me ya sa Sinawa suka hada kansu wajen raya kasa bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin?
A karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20, a wancan lokaci Sin na fama da mulkin mallakar kasashen yamma, bayan namijin kokarin da masu juyin juya hali suka yi, a karshe an zabi hanyar kwaminisanci, kuma marigayi Mao ya jagoranci jama’a wajen kawo karshen mulkin mallaka, da samun ‘yancin kai, tare da kafa jamhuriyyar jama’ar kasar Sin.
An sa kalmar “jama’a” a cikin sunan kasar saboda bayyana hakkin jama’a, wato sanya moriyar jama’a a gaban komai, wanda shi ne burin da jam’iyyar JKS ke neman cimmawa tun daga farko. Yin gwagwarmayar kare hakkin jama’a da tabbatar da zaman alheri ga jama’a, shi ne dalilin da ya sa jam’iyyar ke samun goyon bayan jama’a matuka, kuma dalilin da ya sa jama’a suke amsa kiran shugaba Mao Zedong.
Bayan kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin, jam’iyyar JKS ba ta sauya muradunta ba ko kadan, ta ci gaba da mai da moriyar jama’a a gaban komai. Sai dai a lokacin, Sin ta fusakanci koma baya matuka, saboda haka, gwamnatin kasar ta fitar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, matakin da ya fara fitar da wasu mutane daga kangin talauci, wadanda kuma daga bisani suka jagoranci karin al’umma don su samu wadata tare.
Ban da wannan kuma, gwamnatin na dukufa kan kawar da kangin talauci a duk fadin kasar, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba. Lokacin da na yi aiki da Najeriya, a yayin wani taro, jami’an ofishin jakadan Sin dake kasar sun baiwa wasu jami’an majalisar dokoki wani littafi mai taken “Kawar da talauci” da shugaba Xi Jinping ya rubuta, lokacin da ya yi aiki a Ningde na lardin Fujian a matsayin direktan wurin.
Wani dan majalisar da ya karbi littafin ya bayyana cewa, Najeriya na matukar bukatar dabarun kawar da talauci da Sin take da su. Babu shakka abin mamaki ne yadda jam’iyyar JKS ta kai ga fitar da kasar da ke da al’umma masu dimbin yawa daga kangin talauci. Wannan shi ne ya bayyana ingancin tsarin siyasar kasar Sin, wato hadin kan jama’a da aiwatar da manufofi a duk fadin kasar ba tare da gamuwa da wani cikas ba.
Daga baya, ya tambaye ni, ko na shiga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko a’a. Na amsa masa cewa: ban shiga jam’iyyar ba tukuna. Ya yi mamaki sosai, saboda ganin yadda jam’iyyar take samun goyon bayan jama’a sosai, amma ni ban zama ‘yar jam’iyyar ba tukuna. Na yi masa bayani da cewa, a matsayina na ‘yar kasar Sin, ina da hakkin shiga jam’iyyar ko a’a. Idan manufofin da gwamnati ke dauka sun inganta zaman rayuwata, to zan goyi bayan ta, duk da cewa ni ba ‘yar jam’iyyar ba ce.
Ban da wannan kuma, dukkan ‘yan jam’iyyar na karkashin idon jama’a. Ina fari ciki sosai da sa ido kansu. Wadannan ‘yan majalisar sun yi murmushi suna cewa, wannan shi ne dalilin da ya sa jam’iyyar JKS take yawan samun goyon baya daga jama’a, har ma wadanda ba su zama mambobinta ba.
Kwanan baya, na zanta da ministan zirga-zirgar jiragen saman kasar Najeriya Hadi•Sirika, wanda ya gaya min cewa: “Tattalin arziki da zaman al’ummar kasar Sin sun samu ci gaba sosai karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping. Jama’a na jin dadin zaman rayuwarsu. Ya kamata, wata nagartacciyar jam’iyya ta biya bukatun jama’a, da kyautata zaman rayuwarsu, wanda hakan hanya ce daya tilo, ta samun goyon bayansu cikin dogon lokaci. Na tuntubi wasu ‘yan jam’iyyar, dukkansu suna kishin kasa da son aiki, abin da ya sa suka zama kashin bayan bunkasuwar kasar Sin.” Haka ne, bisa nazarin da kwalejin Kennedy na jami’ar Harvard ya yi, yawan mutane dake goyon bayan jam’iyyar JKS yana da matukar yawa, inda ya kai kashi 90%. Jam’iyyar JKS ta jagoranci jama’arta wajen samun bunkasuwa bisa tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin. Kuma kullum tana daukar matakan tabbatar da moriyar jama’a da farfado da al’umma, kuma ta mai da muradun jama’a a gaban komai, tare da bautawa jama’a bisa iyakacin kokarinta. Shin ko akwai wani mutum da ba ya son jam’iyya irin wannan ba?  (Amina Xu)