logo

HAUSA

Dalibai ‘yan Afirka da suka samu wasika daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin

2021-06-29 13:35:12 CMG

Dalibai ‘yan Afirka da suka samu wasika daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin_fororder_20210629-bayani-dalibai-Bello-1    Dalibai ‘yan Afirka da suka samu wasika daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin_fororder_20210629-bayani-dalibai-Bello-2

A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya samu wata wasika da wasu dalibai ‘yan kasashen waje suka rubuta masa, daga bisani shi ma ya aike musu da wata wasika, inda ya bukaci daliban da su kara fadada sanin su game da kasar Sin.

A kwanan baya, wasu dalibai ‘yan kasashen waje 45, dake karatu a jami’ar Peking ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kasashe 32, sun rubuta wata wasika ga shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Mista Xi Jinping, inda suka taya shi murnar cikar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin shekaru 100 da kafuwa. Daga bisani sun samu wata wasikar da shugaba Xi Jinping ya rubuta musu, abun da ya faranta ransu matuka.

“Na yi farin ciki sosai, kuma ina alfahari sosai. Shugaba Xi Jinping ya rubuta mana wata wasika, duk da cewa yana shan aiki matuka. Hakan ya burge mu, kana yana da ma’ana sosai.”

Saurayin da ya yi wannan magana, sunansa Joseph Mendo’o, wanda ya zo daga kasar Kamaru. Ya fara koyon harshen Sinanci a kwalejin Confucious dake cikin jami’a ta biyu ta Yaounde a shekarar 2014, daga baya ya samu cin jarrabawar harshen Sinanci ta HSK a mataki na 5 cikin shekara guda daya, inda ya iya karanta jaridun Sinanci, da kallon shirye-shiryen bidiyo na Sinanci, da yin jawabi da Sinanci. Wannan nasarar da ya samu ta shaida kokarin da ya yi a fannin koyon harshen Sinanci.

Daga bisani, Mendo’o ya cimma burinsa na yin karatu a cikin jami’ar Peking ta kasar Sin. Kana a halin yanzu yana karatun digirin digirgir a kwalejin huldar kasa da kasa na jami’ar.

A cewarsa, wasu sabbin dabarun da kasar Sin ta gabatar don kawar da talauci a cikin gidanta, da karfafa hadin gwiwar kasashe daban daban a kokarin dakile annobar cutar COIVD-19 a duniya sun burge shi sosai.

“Kasancewar na zo daga nahiyar Afirka, na fi mai da hankali kan fannonin rage da talauci, da raya tattalin arziki, da dai sauransu. Mu ma mun ambaci batun rage talauci a cikin wasikar da muka aikewa shugaba Xi. Ko da yake kasar Sin ita ma tana kokarin dakile cutar COVID-19, duk da haka ta samar da tallafi ga sauran kasashe, wannan shi ma ya burge mu matuka.”

Donglona Thomas, wani dalibi ne da ya zo daga kasar Chadi, wanda shi ma yake cikin daliban da suka rubuta wasika ga shugaba Xi. A shekarar 2012, Tomas ya halarci jarrabawar neman shiga jami’a a kasarsa ta Chadi, inda makin da ya samu ya zama mafi yawa cikin na dukkan daliban da suka halarci jarrabawar, ta yadda ya samu damar karatu a kasar Sin. Yanzu haka shi ma yana kokarin karatun digirin digirgir, a kwalejin nazarin huldar kasa da kasa dake jami’ar Peking ta kasar Sin. A cewarsa, dalilin da ya sa shi da abokansa suka rubuta wannan wasika, shi ne taya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin murna, gami da nuna godiya ga jama’ar kasar.

“Kasar Sin na ta samun ci gaba karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Kana mun gane wa idanunmu yadda kasar Sin take daukar takamaiman matakai, don dakile annobar cutar COVID-19, da yadda take kula da jama’arta, gami da mu dalibai na kasashe daban daban. Mun rubuta wannan wasika ga shugaba Xi Jinping, don taya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin murnar cikarta shekaru 100 da kafuwa. Sa’an nan muna son bayyana godiya ga gwamnatin kasar Sin kan yadda take ba mu kulawa sosai. Ban da wannan kuma, mun bayyana wa shugaba Xi wasu abubuwan da muka gani a kasar Sin, da abubuwan da muke ji a zukatan mu.”

A cewar Mendo’o da Thomas, yadda jam’iyya mai mulki ta kasar Sin, wato jam’iyyar Kwaminis ta kasar, take mai da moriyar jama’a gaban komai, wani abu ne da ya burge su, kana babban dalili ne da ya sa kasar Sin ke samun ci gaba cikin sauri.

Ban da wannan, a halin yanzu suna kokarin koyon ilimi da fasahohin kasar Sin, ta yadda a nan gaba za su koma kasashensu na asali, tare da raya su bisa wadannan fasahohin da suka koya. (Bello Wang)

Bello