An kammala zagayen farko na gasar cin kofin kasashen turai! ‘Yan wasa da kungiyoyi sun kafa tarihi
2021-06-29 16:28:11 CRI
Yanzu haka dai an kammala zagayen rukunoni na gasar cin kofin turai na 2020. A zagayen na farko dai an zura kwallaye 28 a wasanni 12 da aka buga, wato daidai da kimanin kwallaye 2.34 ke nan a duk wasa.
‘Yan wasa 3, wato Sigg, da Ronaldo da Lukaku, sun ci kwallaye biyu biyu a wasannin. Kungiyoyin kwallon kafar da suka shaba taka rawar gani a gasar wato Italiya, da Netherlands, da England, da Faransa sun lashe wasannin su.
A yayin wasannin zagayen na farko na wannan gasa, an kafa wasu tarihi masu gamsarwa. Misali a wasan farko, dan wasan bayan kasar Turkiyya Demiral, ya jefa kwallo a ragar kasarsa, wadda ta kasance irin ta ta farko da aka ci a gasar cikin kofin na kasashen turai. Kaza lika yayin wasan Scotland da Czech Republic, dan wasan gaban Czech Sigg ya jefa kwallo a raga ta hanyar buga kwallo daga tazara mai nisa, kwallon da aka tabbatar ita ce mafi nisa da aka ci a gasar wato daga nisan mita 45.4.
Kungiyar Ingila ita ma ta karya matsayin bajimtarta, inda ta doke Croatia da ci daya da nema. Wannan nasara ta kawar da rashin nasarar da Ingila ta jima tana fuskanta a wannan gasa, domin kafin wannan lokaci bata taba lashe wasan farko na bude gasar ba. A baya Ingila ta buga kunnen doki 5 ta kuma yi rashin nasara 4.
Cikin ‘yan wasan da suka jima suna taka rawa a gasar, Ronaldo ya sake kafa tarihi, inda a wannan karo ya ciwa Portugal kwallo, kana Portugal din ta kammala wasan da nasara kan Hungary da ci 3 da nema. Yanzu haka Ronaldo na da kwallaye 11 a wannan gasa, inda ya zarce yawan kwallayen da Platini ya ci a gasar. A lokaci guda kuma, ya zamo dan wasan kwallo na farko a tarihi da ya buga gasar cin kofin kasashen turai sau 5 ya kuma ci kwallaye a wasannin.
Pandev, mai shekaru 37 da kwanaki 321, tare da kungiyarsa ta arewacin Macedonia, sun shiga wannan gasa a karon farko. Ya kuma kafa tarihin kasancewa dan wasa wanda ba mai tsaron gida ba, mafi yawan shekaru da ya buga wannan gasa. Yayin da dan wasan Ingila Behring Uhm mai shekaru 17 dake buga tsakiya ya zamo dan wasa mafi karancin shekaru da ya fara buga wannan gasa a bana.
Kari kan hakan, Sifaniya ta tashi wasan ta da Sweden kunnen doki ba ci. A wannan karo Sifaniya ta kafa tarihin nuna bajimtar rike kwallo da kaso 75%, yayin da Sweden ta rike kwallo da kaso 25%, inda dukkanin su suka kafa tarihi a wannan fanni a gasar. Kari kan hakan, ‘yan wasan Sifaniya sun mika kwallo tsakanin su har sau 852, yayin da na Sweden suka mika kwallo sau 103, wanda shi ma karya bajimtar da aka taba samu a wannan gasa ne cikin wasa guda.
A nata bangare, Finland ta taki sa’a a wasan da ta buga na wannan gasa. Inda ta doke Denmark da ci 1 da nema, ta hanyar buga kwallo sau daya kacal zuwa ragar Denmark. Yanzu dai Finland din ce ke da tarihin buga kwallo sau daya zuwa ragar abokiyar karawa a wannan gasa, ta kuma lashe wasan da wannan kwallo daya tilo. A daya bangaren kuma, wannan ne karon farko da Finland ta shiga wata babbar gasar kasa da kasa ta kwallon kafa, inda a baya bata taba zuwa gasar cin kofin duniya, ko na kungiyoyin kasashen turai ba. Ko shakka ba bu Finland ta taki sa’a!
Yanzu dai an fara wannan gasa, an kuma fara ta cikin nishadi da kayatarwa. Yayin da aka fara wannan gasa ta cin kofin kwallon kafar kasashen turai ta 2020, an riga an buga wasanni 12 masu ban sha’awa, Ana kuma hasashen ‘yan kallo za su kalli karin wasanni masu kayatarwa, yayin da gasar ke kara nisa da armashi.