logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Japan ta tafiyar da batun tilastawa mata karuwanci bisa gaskiya da sanin ya kamata

2021-06-29 10:38:15 CRI

Kasar Sin ta bukaci Japan ta tafiyar da batun tilastawa mata karuwanci bisa gaskiya da sanin ya kamata_fororder_fdbf00cb8f384d1c99c64ff6b59fd004

Kasar Sin ta bukaci Japan ta tafiyar da batun tilastawa mata karuwanci da sojojinta suka yi yayin yakin duniya na II, bisa gaskiya da sanin ya kamata.

Ministan ofishin kasar Sin a MDD da ke Geneva, Jiang Duan ne ya yi kiran, yayin zama na 47 na hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta MDD dake gudana a Geneva.

Yayin zaman muhawara da aka yi a jiya, Dubravka Simonovic, wakiliyar musammam ta MDD kan cin zarafin mata, ta bayyana cikin rahotonta cewa, yayin Yakin Duniya na II, sojojin Japan sun yi wa mata masu yawa fyade a yankin Nanjing na kasar Sin, kana sun tilastawa mata karuwanci a kasashe da dama.

A cewar Jiang Duan, har zuwa yanzu, mutane da dama a Japan na kokarin musanta laifuffukan da sojojin kasar suka aikata, ciki har da kisan kiyashi a Nanjing da tilastawa mata karuwanci, a yunkurinsu na musantawa da kuma gyara tarihin zalunci.

Har ila yau, yayin zaman na jiya, wakilin kasar Koriya ta Kudu, ya ayyana damuwa game da batun, yana mai cewa kyamar da ake nunawa matan da aka tilastawa karuwanci, da kuma kyale masu laifin ba tare da hukunta su ba, na kara kawo illa da ta’azzara wahalar da matan suke sha. (Fa’iza Mustapha)