logo

HAUSA

Kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha zai kara taimaka ga tsaron duniya

2021-06-29 15:37:36 CRI

Kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha zai kara taimaka ga tsaron duniya_fororder_AA

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari ta kafar bidiyo tare da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda shugabannin biyu suka fitar da sanarwa cikin hadin-gwiwa, da yanke shawarar kara wa’adin aikin yarjejeniyar sada zumunta da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha. A yayin da cutar COVID-19 ke kara haifar da tasiri da takara tsakanin kasa da kasa, kara wa’adin yarjejeniyar, ba shaida babban kuzarin da dangantakar abota tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni kadai take ba, har ma da taimakawa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya baki daya.

A matsayin su na zaunannun kasashe membobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Sin da Rasha sun cimma matsaya daya kan wasu muhimman batutuwa da dama, ciki har da “irin zaman oda da duniya take bukata”, da kuma “irin ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya na ainihi ”.

Kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha zai kara taimaka ga tsaron duniya_fororder_BB

Sin da Rasha sun jaddada kiyaye tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, da zaman doka da oda bisa tushen dokokin duniya, da goyon-baya gami da aiwatar da ainihin ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban, da ci gaba da yayata ra’ayin shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba da demokuradiyya da tabbatar da adalci da ‘yanci, a wani kokari na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, Rasha na bukatar kasar Sin mai ci gaba da zaman karko, Sin ma na bukatar kasar Rasha mai karin karfi da nasarori. Duk duniya tana kuma bukatar gudummawar kasashen biyu na sanya sabon kuzari da kawo zaman lafiya. Ana ganin cewa, a yayin da ake fuskantar matsaloli da dama a halin yanzu, kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha, zai kara samar da tabbaci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk duniya. (Murtala Zhang)