Dakta Agaba Halidu: Muhimmiyar Rawar da Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Ta Taka A Shekaru 100
2021-06-29 14:50:26 CRI
Ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara ta 2021 ita ce ranar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS. Ko shakka babu, Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannoni daban daban cikin wadannan shekaru da suka gabata karkashin jagorancin JKS.
A kan haka ne Murtala Zhang ya zanta da Dakta Agaba Halidu, na sashen nazarin kimiyyar siyasa da dangantakar kasa da kasa a jami’ar Abuja dake tarayyar Najeriya. Ya fara ne da yin tsokaci game da irin rawar da JKS ta taka ga fagen siyasar kasar Sin gami da manyan sauye-sauyen da aka samu na ci gaban kasar cikin shekaru 100 da suka gabata. Masanin ya ce, shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar ya kasance a matsayin muhimmiyar tafiya mai cike da dogon tarihi bisa la’akari da irin rawar da ta taka wajen bada jagoranci ga al’umma da yadda jam’iyyar ta kasance a matsayin alkibla wajen taimakawa gwamnati don tafiyar da sha’anin shugabancin al’umma, ya ce a ra’ayinsa jam’iyyar ta taka gagarumar rawar da ya dace a yaba mata duba da irin namijin kokarin da ta yi wajen sauke nauyin dake bisa wuyanta ta fuskar rungumar al’amurran dake shafar rayuwar al’ummar kasa da ci gaban al’ummar, ko shakka babu jam’iyyar ta yi namijin kokari a matsayinta na jam’iyya wajen zaburar da al’ummar kasar wato Sinawa.
Ban da wannan kuma JKS ta kasance wani muhimmin bangare wanda ta wayar da kai ga shugabannin siyasa wato shugabannin Sinawa. Ban da wannan kuma jam’iyyar JKS ta kasance jam’iyyar dake kokarin neman hanyoyin kyautata moriyar kasa musamman moriyar dake shafar al’ummun Sinawa. Wadannan na daga cikin muhimman rawar da JKS ta taka a cikin wadannan shekaru 100 da suka gaba. Ya ce duba da wadannan batutuwan da ya zayyana hakika a bayyane take jam’iyyar JKS ta yi namijin kokarin ciyar da al’umma gaba.
Game da muhimman ci gaban da kasar Sin ta samu karkashin jagorancin jam’iyyar JKS musamman a fannonin yaki da talauci, kimiyya da fasaha, da yadda aka samu gagarumin ci gaba wajen kyautatuwar zaman rayuwar al’ummar Sinawa, masanin ya ce:
“Ni a matsayina, na lura kamar yadda na ambata tun da farko, shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya zama dole a jinjinawa jam’iyyar, idan muka dauki fannonin daya bayan daya, za mu iya cewa an yi namijin kokari idan ka duba musamman ga fannin yaki da fatara, ina tunanin a bisa yadda na kalli batun akwai maganganu masu tarin yawa game da al’ummun Sinawa musamman idan muka yi dubi gabanin shekarun 1949, da shekarun 1978, a wancan lokacin abin da aka fi bayyanawa shi ne ana daukar kasar Sin a matsayin mai fama da koma bayan ci gaba a nahiyar Asiya, saboda lura da alkaluman dake nuna matakin koma bayan ci gaba da take da shi a lokacin ana bayyana ta a matsayin kasar dake da koma bayan ci gaba kuma daya daga cikin wadannan matsaloli shi ne talauci.”
Masanin ya ce, amma ta hanyar amfani da manufofin jam’iyyar JKS a cikin dogon lokaci, idan za a iya tunawa a shekarar 2020 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta ayyana nasarar da ta samu na yin ban kwana da talauci sakamakon tsame kafatanin al’ummarta daga kangin talauci. Ya ce abin da yake kokarin bayyanawa shi ne jam’iyyar JKS ta taka gagarumar rawa wajen yaki da talauci a kasar, bayanai sun bayyana karara cewa kafin shekarar 2000 akwai kauyuka kimanin 128,000 dake rayuwa a yanayin kangin talauci, akwai kuma yankuna da dama dake fama da matsalar talaucin, to sai dai yayin da mahukuntan kasar suka dukufa wajen amfani da hikimomin da magabatan suka bullo da su game da yadda za a kyautata rayuwar Sinawa, sai shugabannin suka aiwatar da manufofi gami da gabatar da shawarwari karkashin kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato sun aiwatar da hakikanin tsare tsare da manufofin jam’iyyar don haka kwamitin tsakiyar JKS ya samu nasarar aiwatar da manyan sauye-sauye tare kuma da aiwatar da muhimman manufofi gami da dabaru wadanda suka taimakawa kasar ta samu manyan nasarorin wanda a halin yanzu batun kangin talauci ya zama sai tarihi a kasar.
Sai dai masanin ya aza wata tambaya, inda ya ce, shin ta yaya ne kasar Sin ta cimma wannan nasara?
Ya ce, “bisa ga abin da na gani, bayanai sun nuna cewa, a cikin bayanan tarihi an tabbatar da cewa akwai manyan dabarun da aka yi amfani da su, kuma daya daga cikinsu shi ne, game da abin da na karanta a tarihi shi ne, hujjojin da ake da su sun bayyana cewa da farko an fara ne da duba kididdigar adadin iyalan dake cikin yanayin talauci, daga nan aka tsara manufofin bisa ilmin bayanan da ake da su, domin kuwa ba zai taba yiwuwa a tsara wani shiri kai tsaye ba tilas ne sai an tsara manufar daga nan sai a kai zuwa matakin aiwatar da manufar, jam’iyyar JKS ta jagoranci sanya ido wajen tsarawa da kuma aiwatar da wadannan manufofi da tsare-tsaren, kuma daga cikinsu kamar yadda na ambata shi ne farawa da tantance iyalai masu fama da talauci kuma JKS ta yi rejistar wadannan magidanta domin tantance hakikanin masu fama da talaucin, domin idan kana son samar da kowane irin ci gaba wajibi ne sai an tantance alkaluman bayanai, don haka JKS ta yi namijin kokari wajen tattara alkaluman daidaikun jama’a masu fama da talauci.”
Ya ce wani batu kuma dake da muhimmanci shi ne, bayan tattara alkaluman, JKS ta tsara yadda za a tura jami’ai zuwa yankunan da abin ya shafa masu fama da talauci, daga nan kuma sai JKS ta kara kaiwa ga mataki na gaba wato samar da kudaden aiwatar da shirin, saboda idan kana son tsame mutane daga talauci tilas ne sai an samar da kudaden aiwatar da shirin, kuma dole ne a samarwa mutane kyakkyawan muhallin da zai taimaka wajen cimma nasarar abin da aka sanya gaba, misali, samar da hanyoyin bayar da rancen kudaden masu rangwame da samar da bankunan bada rance don raya kananan sana’oi. Kuma alkaluman bayanai sun nuna cewa, an samar da dimbin kudade ga mutane magidanta masu fama da talauci, kuma an yi amfani da kudaden wajen shirye-shiryen dake shafar samar da ayyukan yi, da bayar da horo, daga karshe miliyoyin mutane ne suka ci gajiyar shirin wajen samun ayyukan yi, kana shirin ya taimaka matuka wajen rage yanayin kangin talauci.
Ban da wannan kuma, JKS ta bullo da tsarin bada ilmi a yankuna masu fama da talauci wadanda ke fama da matsalar karancin ci gaba, an samar musu da kyakkyawan muhallin da zai ba su damar samun ilmi, ban da wannan kuma, an samar da tsarin bada tallafi a fannin kiwon lafiya, da yin kwaskwarima ga gidajen mutane marasa sukuni, da gina hanyoyin mota, kuma aikin gina hanyoyin mota yana da matukar muhimmanci musamman yana taimakawa mazauna yankunan karkara wajen samun saukin fitar da amfanin gonar da suka noma zuwa sauran yankuna. Ban da wannan kuma JKS ta samar da tsarin samar da ruwan sha musamman ga wadannan yankuna masu fama da talauci wadanda suke fuskantar wahalhalu wajen samun ruwan sha, wadannan suna daga cikin muhimman ayyukan da JKS ta aiwatar musamman karkashin shirin yaki da talauci kuma wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ta samu gagarumar nasara inda a shekarar 2020 da ta gabata kasar ta ayyana cewa a’lummarta sun yi ban kwana da kangin talauci.
Idan muka koma batun ci gaban kimiyya da fasaha kuwa, masanin ya ce babu shakka CPC ta yi manijin kokari a fannin ci gaban kimiyya da fasaha a kasar Sin bayan aiwatar da manufar sauye-sauye a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, idan ana batun manufar sauye-sauye a gida wanda marigayi Deng Xiaoping ya kaddamar tare da sanya ido ta taka gagarumar rawa a fannin bunkasa ilmin kimiyya da fasaha a kasar Sin, wanda karkashin wannan manufar JKS ta yi kokarin kafa cibiyoyin raya tattalin arziki, kana an kafa rukunin bunkasa ci gaban tattalin arziki da fasaha. Ya ce wadannan na daga cikin muhimman ayyukan raya kasa da jam’iyyar JKS ta bullo da su inda a yau kasar Sin ta samu shahara a duniya, a halin yanzu kasar Sin ta kasance ta biyu a fannin ci gaban tattalin arziki a duniya bayan kasar Amurka.
Masanin ya yi fashin baki tare da dunkule ci gaban da JKS ta samu a cikin shekaru 100 da suka gabata, inda ya ce:
“A jimlace bayan cimma nasarar kawar da talauci, da bunkasa ci gaban al’umma ta fuskar raya ci gaban fasahohi, da kyautata zaman rayuwar al’ummar Sinawa, a halin yanzu, al’ummar Sinawa sun samu damammakin cin moriyar muhimman abubuwan bukatu na rayuwarsu sannan fasahohi sun kara taimakawa wajen ci gaban rayuwar al’ummar. A dunkule wannan yana kara bayyana yadda rayuwar Sinawa ta sauya ta fuskar samun ci gaba don haka tilas ne a yabawa jam’iyyar JKS.”
Game da batun yaki da annobar COVID-19 kuwa, masanin ya bayyana cewa, jam’iyyar JKS da gwamnatin Sin abokan aikin juna ne, yayin da aka samu barkewar annobar, bangarorin biyu sun yi aiki tare wajen yaki da annobar, inda suka bullo da muhimman dabaru wajen dakile yaduwar annobar. Ya kara da cewa:
“Idan ana maganar jam’iyyar JKS ana maganar gwamnatin kasar Sin ne, don haka duk wasu matakai da kokarin da gwamnatin Sin take yi wajen yaki da annobar COVID-19, kamar sanya dokar kulle, da yin amfani da fasahohin mutum-mutumi, da sauran fasahohin yaki da cutar za mu iya cewa a fakaice kamar jam’iyyar JKS ce ta gudanar kasancewar ita ce kashin bayan jagorancin gwamnatin kasar Sin, don haka fasahohin da Sin ta yi amfani da su sun taimaka wajen kawar da annobar daga kasar, domin ba za a taba iya rabe jam’iyyar JKS da gwamnatin kasar Sin ba don kasar Sin ta samu nasarar dakile annobar cikin kankanin lokaci.”
Haka zalika, masanin ya yi fashin baki game da matakan kasar Sin na kara bude kofarta ga ketare, wanda a cewarsa kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen hadin gwiwa da kasa da kasa, misali yadda kasar Sin take kara hadin gwiwa da kasashe masu tasowa kamar yadda ta kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a takaice, wanda ya kara kyautata alakar Sin da Afrika, ya ce misali, a Najeriya akwai ayyukan more rayuwa masu tarin yawa da aka aiwatar karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika. Don haka, Afrika ta ci moriyar huldar dake tsakaninta da Sin, kana duka bangarorin biyu wato Sin da Afrika sun ci moriyar juna.
Dakta Agaba ya ce, akwai muhimman darrusa masu tarin yawa da suka kamata kasashen Afrika su koya daga kasar Sin, ya ce kasashen Afrika musamman Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ya kamata su koyi darasi daga jam’iyyar JKS.
Ya ce darasi na farko da ya kamata su koya shi ne, kasashe masu tasowa su yi kokarin neman hanyoyi masu yawa na bunkasa ci gaban kasashensu wadanda za su dace da yanayin al’ummarsu, JKS ta aiwatar da tsarin gina kasa wanda ya dace da yanayin al’ummarta, don haka ya kamata tsarin demokaradiyyar kasashen Afrika ya kasance mai cike da ‘yanci kamar tsarin jam’iyyu masu yawa. Ya ce jam’iyyar JKS ta bi hanya mafi dacewa wajen raya ci gaban al’ummarta. Na biyu, abin da ya kamata kasashen Afrika su koya musamman Najeriya shi ne, kamata ya yi kasashen su samar da hukumomi masu karfin fada a ji sabanin daidaikun mutane kasancewar idan aka bar al’amurran a hannun daidaiku za su iya kawo cikas ga hukumomin kuma hakan zai iya haifar da koma bayan ci gaba, kuma burin da ake da shi na samun ci gaba ba za a taba cimma shi ba, jam’iyyar JKS ta kasance mai karfin fada a ji, ta fi karfin daidaikun mutane kuma wannan shi ne ya taimakawa al’ummar Sinawa suka samu gagarumin cigaba, JKS ta shafe shekaru aru-aru tana nan darama tana biyan muradun al’ummar kasar don haka ya dace kasashen Afrika musamman Najeriya su bunkasa hukumomi kamar jam’iyyun siyasa don samun ci gaban kasashen. Na uku, binciken da aka gudanar ya nuna cewa, jam’iyyar JKS tana da manufofi masu karfi, kuma bisa ga wadannan manufofin da aka gada daga magabata ne, kuma idan ana maganar magabata tilas ne a ambaci shugaba Mao Zedong, kuma babbar manufar magabatan shi ne a samar da hanyoyin kyautata al’ummar kasa, wannan shi ne babbar manufar magabata. Don haka akwai darrusa masu yawa da ya kamata kasashe masu tasowa kamar Afrika ya kamata su koya wajen samar da ingantattun manufofi, tilas ne jam’iyyun siyasa su samar da ingantattun manufofin raya kasa da gina al’umma. Na hudu, ya kamata su koyi kyakkyawan shugabanci da sadaukar da kai domin gina ci gaban kasa da al’ummar kasar, misali ba za ka taba iya raba al’ummar Sinawa da jam’iyya ba sakamakon irin shugabancin da take gudanarwa wajen kyautata rayuwar al’umma, wadannan suna daga cikin muhimman darrusan da ya kamata kasashen Afirka su koya daga JKS. (Murtala Zhang/ Ahmad Fagam)